Siyasa Ta Dauki Zafi, An Farmaki Peter Obi da Kwankwaso a Hanyarsu Ta zuwa Wurin Taro

Siyasa Ta Dauki Zafi, An Farmaki Peter Obi da Kwankwaso a Hanyarsu Ta zuwa Wurin Taro

  • An kai wa ayarin motocin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso, hari a Calabar, jihar Cross River
  • Rahotanni sun ce maharan sun jefi motocin da duwatsu da wasu abubuwa, inda wasu daga cikinsu suka lalace
  • ’Yan sanda sun kama wani mutum mai suna Victor Edet Yellow Duke, mai shekara 27, bisa zargin hannu a harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Cross River, Nigeria - Wasu ’yan daba sun kai hari kan ayarin motocin da ke ɗauke da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Alhaji Rabiu Kwankwaso

Maharan sun farmaki ayarin Obi da Kwankwaso ne s daidai mahadar Watt Market Roundabout da ke Calabar, babban birnin Jihar Cross River, a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Atiku da Amaechi sun dura jihar Sakkwato domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ADC

Kwankwaso.
Dan takarar shugavan kasa na NDC, Peter Obi tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Yan daba sun farmaki Obi, Kwankwaso

Leadership ta ruwaito cewa maharan sun jefi ayarin motocin da duwatsu da wasu abubuwa, lamarin da ya haddasa lalacewar wasu motocin da ke cikin ayarin.

Sai dai babu wanda ya samu rauni daga cikin Obi da Kwankwaso da sauran mutanen da ke tare da su.

Harin ya faru ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani otal da ke gaban filin wasa na U.J. Esuene, bayan ziyarar girmamawa da suka kai wa Obong na Calabar.

An shirya gudanar da taron tattaunawa da Peter Obi da Kwankwaso da masu ruwa da tsaki na NDC, magoya bayanta da ’yan takarar jam’iyyar na jihar Cross River.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa yan daban sun farmaki ayarin Obi da kwankwaso nena hanyar zuwa wurin wannan taro a Calabar.

Yan sanda sun dakile rikici a Calabar

Lamarin ya faru ne sa’o’i kaɗan bayan ’yan sanda da sauran jami’an tsaro sun dakile yiwuwae qbarkewar rikici tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki da na NDC a Calabar.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Yan bindiga sun tare magidanci da ya ɗauko gawar matarsa daga jihar Kano

Tun da farko, magoya bayan APC, ciki har da mambobin Ƙungiyar Ƙananan Hukumomin Najeriya (ALGON), sun fito kan tituna da ke zuwa Gidan Gwamnati, inda aka shirya za su gana da Gwamna Bassey Otu.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, ASP Sunday Eitokpah Akata, ya tabbatar da faruwar waɗannan al’amura guda biyu.

Cross River.
Taswirar jihar Cross River da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kakakin yan sandan ya ce rundunar ta ƙara tsaurara matakan sa ido domin hana sake samun tabarbarewar tsaro da karya doka da oda.

Dangane da harin da aka kai wa ayarin motocin NDC, Akata ya bayyana cewa an kama wani mutum da ake zargi da hannu a lamarin.

“An kama wani wanda ake zargi mai suna Victor Edet Yellow Duke, namiji, mai shekara 27,” in ji shi.

Peter Obi zai aiki da Kwankwaso

Kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso idan suka lashe zaɓen 2027.

Ya ce kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya zai kasance cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa za ta ba fifiko, tare da ɗaukar matakan magance matsalolin tsaro da ke barazana ga yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262