2027: Yadda Mutane Suka Rika Rera 'Tinubu Must Go' yayin Tarbar Atiku Ya Ja Hankali
- Magoya bayan ADC sun riƙa rera taken “Tinubu Must Go” yayin ƙaddamar da yakin neman zaben dan shugaban ƙasa na jam’iyyar a Sakkwato
- Masu halartar gangamin sun bayyana goyon bayansu ga Atiku Abubakar tare da nuna rashin gamsuwarsu da gwamnatin Shugaba Tinubu
- An ce ayarin Atiku da tawagarsa ya shafe tsawon lokaci bai isa wurin gangamin ba saboda cunkoson jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Mutane sun rika rera taken “Tinubu Must Go” ma'sna dole a canza Tinubu a kan titin Ilorin da ke cikin birnin Sakkwato a ranar Laraba.
An ruwaito cewa magoya bayan jam’iyyar ADC sun rika rera Tinubu Must Go ne lokacin da suka taru domin ƙaddamar da kamfen dan takarar shugaban ƙasa gabanin babban zaɓen 2027.

Source: Facebook
Yadda aka rika rera 'Tinubu Must Go'
Leadership ta ce magoya bayan jam’iyyar sun riƙa rera wannan kalamai a yayin da suke jiran isowar manyan shugabannin ADC da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.
Taken ya nuna irin adawar da masu halartar taron ke nunawa ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Haka kuma, ya bayyana matsayin magoya bayan ADC game da shugabancin ƙasar da kuma goyon bayan da suke bai wa Atiku a ƙoƙarinsa na neman zama shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Rahotanni sun bayyana cewa da dama daga cikin magoya bayan da suka halarci gangamin sun yi tattaki daga sassa daban-daban na Jihar Sakkwato domin kasancewa cikin mshalarta taron.
Zuwan waɗannan magoya baya daga sassa daban-daban na jihar ya sanya taron zama wata dama ta haɗuwa da bayyana goyon baya ga jam’iyyar ADC da dan takararta, Atiku Abubakar.'0
Magoya baya sun koka kan halin ƙasa
Baya ga nuna goyon baya ga Atiku, taron ya ba magoya bayan jam’iyyun adawa damar bayyana rashin gamsuwarsu da yadda gwamnatin Shugaba Tinubu ke tafiyar da al’amuran ƙasar.
Daga cikin batutuwan da suka fi jawo hankalinsu akwai matsin tattalin arziki, ƙarin tsadar rayuwa da kuma matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar sassan Najeriya.
Gangamin ya kuma zama wani ɓangare na ƙoƙarin ADC na ƙarfafa goyon bayan da take da shi a tsakanin al’umma, musamman a matakin tushe, tare da tattara magoya baya da wayar da kan ’yan Najeriya gabanin babban zaɓen 2027.

Source: Facebook
Ayarin motocin ADC ya makara
Sai dai duk da taron magoya bayan da aka gudanar a kan titin Ilorin, ayarin motocin kamfen ɗin shugaban ƙasa na ADC bai isa wurin taron a kan lokaci na.
Ayarin motocin na kan hanyarsa ne daga filin jirgin sama na Sultan Abubakar III da ke Sakkwato zuwa wurin da aka shirya gudanar da taron.
Rahotanni sun nuna cewa tarin jama’ar da suka yi cincirindo a kan hanyar da ayarin motocin zai bi ne ya jawo tsaikon isowarsa.
Atiku ya nanata alkawurransa
Kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin magance matsalar tsaro da dawo da zaman lafiya a Najeriya idan ya lashe zaɓen 2027.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen a Sokoto a matsayin farkon tafiyar da yaƙin neman ceton Najeriya.
Asali: Legit.ng

