An Bude Wuta ga Magoya bayan ADC yayin da Atiku Ke Kamfen a Sokoto

An Bude Wuta ga Magoya bayan ADC yayin da Atiku Ke Kamfen a Sokoto

  • Ana zargin jami’an Community Guards sun harbi wasu mutane biyu da ake kyautata zaton magoya bayan ADC ne a kan hanyar Sokoto zuwa Wurno
  • Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne bayan jami’an tsaron sun tare hanya tare da hana motocin magoya bayan jam’iyyar wucewa
  • Rundunar ’yan sandan Sokoto ta ce ba ta samu rahoton faruwar harbin ba, don haka ba ta iya tabbatar da lamarin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Ana zargin wasu jami’an rundunar Community Guards ta Jihar Sokoto sun harbi mutane biyu da ake kyautata zaton magoya bayan jam’iyyar ADC ne a kan hanyar Sokoto zuwa Wurno ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamban 2026.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar takun saka ta siyasa a jihar, gabanin gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC.

Kara karanta wannan

EFCC ta bankado haramtacciyar matatar mai ta 'yan kasar waje cikin daji

Ana zargin an harbi mambobin ADC a Sokoto
Magoya bayan jam'iyyar ADC a wajen kamfen a Sokoto Hoto: Walin Sokoto Media Team
Source: Facebook

Rahotan jaridar Vanguard ya ce jami’an sun tare hanyar da ta haɗa babban birnin Sokoto da yankin gabashin jihar, lamarin da ya tilasta wa motocin da ke ɗauke da magoya bayan jam’iyyar komawa baya.

Yadda aka yi zargin harbin magoya bayan ADC

An ce mutanen biyu da aka harba na cikin waɗanda ke kan hanyarsu ta zuwa wurin gangamin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar.

Shaidun gani da ido sun yi zargin cewa harbin ya biyo bayan saɓani tsakanin mutanen da ke cikin wata mota da ke ɗauke da magoya bayan jam’iyyar da jami’an Community Guards.

A cewarsu, jami’an sun buɗe wuta yayin takaddamar, inda harsasai suka samu mutane biyu. Rahotannin sun ce an garzaya da waɗanda suka samu raunukan harbin bindiga zuwa asibiti domin ba su kulawar likitoci.

Lamarin ya jawo damuwa kan tsaron magoya bayan jam’iyyun siyasa da kuma ’yancin zirga-zirgar jama’a yayin gudanar da harkokin yaƙin neman zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

El Rufai ya aiko sako ga masoya da magoya baya kan 'yan takarar da za su zaba a 2027

Jami’an Civilian JTF sun shiga tsakani

Wata majiya ta bayyana cewa motocin da ke cikin ayarin Sanata Ibrahim Lamido, mai kula da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na ADC a Sokoto, sun fuskanci matsala a shingen binciken jami’an tsaro.

Majiyar ta ce sai da jami’an Civilian JTF da ke cikin ayarin Lamido suka shiga tsakani kafin jami’an shingen su ba motocin damar wucewa.

Wannan sabon lamari ya faru ne a lokacin da ake samun rashin jituwa tsakanin jam’iyyar ADC da wasu jami’an tsaro a jihar.

Rundunar ’yan sanda ta ce ba ta samu rahoto ba

Da Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya ce har yanzu rundunar ba ta samu wani bayani kan zargin harbin ba.

Ya bayyana cewa saboda rashin samun rahoton lamarin, ba zai iya tabbatar da cewa harbin ya faru ba.

"Ban samu wannan rahoton ba, amma zan bincika." In ji shi.

Kara karanta wannan

An fara batun Tinubu ya je Umrah ne don neman kuri'un 'yan Arewa, hadiminsa ya magantu

ADC na taro a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Atiku ya yi alkawura ga 'yan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi alkawura ga 'yan Najeriya.

Atiku ya yi alƙawarin kawo ƙarshen matsalar tsaro, dawo da fata ga ’yan Najeriya da kuma sauƙaƙa tsadar rayuwa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng