Nafiu Bala Ya Sake Kalubalantar Atiku, Ya Kafa Kwamitin Kamfen na 2027

Nafiu Bala Ya Sake Kalubalantar Atiku, Ya Kafa Kwamitin Kamfen na 2027

  • Tsagin jam'iyyar ADC ɓangaren da Nafiu Bala ke jagoranta ya sanar da kafa kwamitin yaƙin neman zaɓe na ƙasa gabanin zaɓukan 2027
  • Ana sa ran kwamitin zai daidaita harkokin yaƙin neman zaɓe a faɗin ƙasar nan, da kuma tattara ‘yan Najeriya domin goyon bayan tsagin ADC
  • Bisa sanarwar da ɓangaren ya fitar, kwamitin yaƙin neman zaɓen na ƙasa zai yi aiki ne a ƙarƙashin jagorancin shugaban jam'iyyar na ƙasa Nafiu Bala Gombe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja — Ɓangaren jam'iyyar ADC karkashin jagorancin Nafiu Bala ya dauki sabon mataki na shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 ta hanyar kafa kwamitin yaƙin neman zaɓe na ƙasa.

Wannan cigaban na zuwa ne a daidai lokacin da manyan jam'iyyu da kungiyoyin siyasa ke cigaba da tsara matsayarsu gabanin babban zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2027: Ana zargin wasu ƙusoshin APC sun fito da kudi don ruguza shirin hadewar yan adawa

Nafiu Bala Gombe
Nafiu Bala mai jagorantar tsagin ADC. Hoto: Nafiu Bala
Source: Twitter

A sakon da ya wallafa a Facebook, Nafiu Bala ya ce kwamitin zai mayar da hankali kan inganta dabarun yaƙin neman zaɓe, da daidaita ayyuka a dukkan jihohin ƙasar nan, tare da tabbatar da haɗin kan tushe.

Shugabannin kwamitin Nafiu Bala

A sanarwar da jam'iyyar ta fitar, an bayyana cewa kwamitin zai kasance a ƙarƙashin jagorancin shugaban tsagin jam'iyyar na ƙasa, Nafiu Bala Gombe, wanda zai jagoranci harkokin gudanarwa da kuma kafa tubali mai ƙwari na nasara.

Bayanai daga takardun da aka gabatar sun nuna cewa an rarraba mukamai daban-daban a cikin kwamitin don tabbatar da ingantaccen aiki a fannonin gudanarwa, harkokin kuɗi, yaƙin neman zaɓe, da kuma wayar da kan matasa da mata.

Wasu daga cikin manyan jami'an da aka amince da su a matsayin shugabannin kwamitin sun haɗa da Farfesa Chris Uba a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa da kuma Dr. Shamsudeen Barkindo a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

An shirya hallaka Atiku ana tunkarar zaben 2027? APC ta magantu

Haka zalika, an sanya Chief Rufus Ikanmi a matsayin mataimakin shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓe, yayin da Farfesa Ahmed Jidda Balarabe ke riƙe da matsayin babban darakta na kwamitin.

Shugabannin sun hada da:

  1. Farfesa Chris Uba – Dan takarar shugaban kasa
  2. Dr Shamsudeen Barkindo – Mataimakin dan takarar shugaban kasa
  3. Hon. Nafiu Bala Gombe – Shugaban kwamitin kamfen
  4. Chief Rufus Ikanmi – Mataimakin kwamitin kamfen
  5. Farfesa. Ahmed Jidda Balarabe – Darkta Janar na kwamitin kamfen
  6. Florida Gabriel – Mataimakin Darakta Janar
  7. Hon. Bala Sani Kumo – Mataimakin Darakta Janar
Nafiu Bala Gombe
Shugaban tsagin ADC, Nafiu Bala. Hoto: Hon. Nafiu Bala
Source: Facebook
  1. Mohammed Abdulkadir Dukku – Arewa maso Gabas
  2. Alh. Suleman S. Hassan – Arewa ta Tsakiya
  3. Hon. Nurudeen Lawal Chindo – Arewa ta Yamma
  4. Alh. Abdulwasiu O. Kayode – Kudu maso Yamma
  5. Prince Richardson Ifeanyi Obiora – Kudu maso Gabas
  6. Chief Thomas D. Arthiavbere – Kudu Maso Kudu

APM ta soki Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa kwamitin yaƙin neman zaɓen Makinde/Daura (MDPCO) tare da jam'iyyar APM sun buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fito ya fuskanci 'yan Najeriya a dukkan jihohi ko kuma ya janye aniyarsa ta sake takara.

Kara karanta wannan

Mawakin siyasa ya watsa wa Abba Kabir kasa a ido kan saka shi a kwamitin kamfe

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ba zai je kowace jiha kamfen ba saboda zai zauna a Abua ya cigaba da gyara Najeriya.

Sai dai jam'iyyar APM ta masa raddi mai zafi da cewa haka ba za ta sabu ba, inda ta bukaci ko ya shirya tafiya kowace jihar ko kuma ya hakura da takarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng