Yadda Dogo Gide Ya Zama Alaƙaƙai ga Kungiyar IS a Arewacin Najeriya

Yadda Dogo Gide Ya Zama Alaƙaƙai ga Kungiyar IS a Arewacin Najeriya

  • Wani masani kan harkokin tsaro ya ce shugaban ’yan bindiga, Dogo Gide, ya kawo cikas ga yunƙurin faɗaɗar ƙungiyar IS a Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Ya bayyana cewa mayaƙan IS sun sha kaye a hannun Dogo Gide bayan sun yi ƙoƙarin mamaye yankunan da yake iko da su
  • Ƙungiyar IS ta kwace sansanoni, makamai da motoci daga wasu ’yan bindiga da suka ƙi shiga cikinta a Zamfara da Sakkwato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Wani fitaccen jagoran ’yan bindiga, Dogo Gide, ya zama babban ƙalubale ga yunƙurin faɗaɗar ƙungiyar Islamic State Sahel Province (ISSP) a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa Dogo Gide ya yi wa ƙungiyar asarar mayaƙa, lamarin da ya tilasta wa wasu daga cikin mayakanta ja da baya daga yankunan da yake iko da su.

Kara karanta wannan

Jerin 'yan Najeriya 4 da suka lashe kujeru daban daban a zaɓen Amurka, na 5 na hanya

Yadda Dogo Gide ke jawo matsala ga kungiyar IS a Arewa
Dan bindiga, Dogo Gide da hafsan sojoji, Laftanar kanal Waidi Shaibu. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Wani masani kan harkokin tsaro, Brant Philip, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba, 2026.

Yadda IS ke ƙoƙarin faɗaɗa ikonta a Arewa

Philip ya ce a cikin shekaru biyu da suka gabata, ƙungiyar ISSP ta sha tuntuɓar ƙungiyoyin ’yan bindiga a jihohin Sakkwato, Zamfara da Neja.

Ya bayyana cewa manufar ƙungiyar ita ce shawo kan ’yan bindigar su miƙa wuya, su tuba tare da shiga cikinta domin taimaka mata wajen yaɗa manufofinta.

A cewarsa, wasu ƙungiyoyin ’yan bindiga a Zamfara da Sakkwato sun amince da tayin, inda suka shiga cikin ƙungiyar, yayin da wasu suka ƙi amincewa.

Masanin ya ƙara da cewa mayaƙan IS sun yi galaba a kan wasu ƙungiyoyin ’yan bindiga a arewacin Zamfara, inda suka ƙwace sansanoninsu, makamai da motocinsu.

Dogo Gide ya hana kungiyar IS sakat
Taswirar jihar Zamfara na daga cikin jihohi da ke fama da matsalar tsaro. Hoto: Legit.
Source: Original

Dogo Gide ya dakile yunƙurin faɗaɗar IS

Sai dai Philip ya ce a tsakiyar shekarar 2026, ƙungiyar IS ta fuskanci babban ƙalubale a yunƙurinta na faɗaɗa iko, bayan ta yi arangama da Dogo Gide.

Kara karanta wannan

Mutanen Tinubu sun fita daga APC sun koma wajen Atiku a ADC

Ya bayyana cewa abin mamaki shi ne, ba sojojin Najeriya ko ƙungiyar JNIM suka kawo mata cikas ba, sai dai Dogo Gide, wanda ya shahara wajen alaƙa da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a wasu lokuta.

A cewar masanin, Dogo Gide shi ne mutum ɗaya tilo da ya iya korar ɓangaren ƙungiyar JAS mai biyayya ga Sadiku daga sansanoninta da ke jihar Neja zuwa yammacin ƙasar.

Sojoji sun cafke na kusa da Dogo Gide

A wani labarin mai kama da wannan, an ji cewa sojojin Najeriya sun kama wani jami’in ISWAP da ake zargi yana aiki tare da shugaban ’yan ta’adda Dogo Gide.

An kuma kama wasu mutane 60 da ake zargi da haɗin gwiwa da ’yan ta’adda a jihar Adamawa yayin aikin da sojoji suka gudanar.

Sojoji sun cafke wasu ’yan ta’adda biyar tare da lalata sansanoninsu a Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.