Aiki Ya Koma Baya: Kotu Ta Rusa Zaɓen Fitar da Gwanin Sanatan APC
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke zaɓen fitar da gwani da ya samar da Sanata Sunday Karimi a matsayin ɗan takarar APC a Kogi ta Yamma
- Mai shari’a Salim Ibrahim ya ce zaɓen da ya samar da Karimi bai samu sa-ido daga INEC ba, don haka ya saɓa wa dokar zaɓe
- Kotu ta umurci APC ta miƙa sunan Bamidele Aro ga INEC, sannan hukumar ta wallafa sunansa a matsayin ɗan takarar jam’iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige Sanata Sunday Karimi a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC mai wakiltar Kogi ta Yamma a zaɓen majalisar dattawa na 2027.
Mai shari’a Salim Ibrahim ne ya yanke hukuncin a ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba, 2026, inda ya soke zaɓen fidda gwani da ya samar da Karimi.

Source: Facebook
Alkalin ya kuma umarci Sanatan da ya daina gabatar da kansa a matsayin ɗan takarar APC a zaɓen majalisar dattawa mai zuwa, cewar Punch.
Dalilin da ya sa kotu ta tsige Sanata Karimi
Rahotanni sun ce kotun ta bayyana cewa Bamidele Aro, wanda ya shigar da ƙara, ya gabatar da isassun hujjoji da suka tabbatar da cewa shi ne ya lashe zaɓen fidda gwani na APC.
Mai shari’a Ibrahim ya ce kwamitin zaɓe na kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) ne ya gudanar da zaɓen da Aro ya lashe, kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanya ido a kansa.
Sai dai alkalin ya ce zaɓen da aka yi ikirarin cewa Karimi ya lashe bai samu sa-ido daga INEC ba, wanda hakan ya sa ya zama ba shi da inganci.
Alkalin ya ce:
"Ba abin mamaki ba ne cewa wanda ake ƙara na uku (INEC) bai ba su sahihin kwafin sakamakon zaɓen ba, duk da cewa wanda ake ƙara na biyu (Karimi) ya nemi hakan ta wasiƙar ranar 15 ga watan Yuni."

Kara karanta wannan
Abba Hikima ya fito da abin da ya kamata mutane su sani kan takarar Pantami da Aminu Gwarzo

Source: Facebook
Umarnin da kotu ta ba APC da INEC
Bayan tabbatar da cewa Aro ya lashe zaɓen fitar da gwanin, kotun ta umarci APC da ta gaggauta miƙa sunansa ga INEC a matsayin ɗan takararta na Kogi ta Yamma.
Haka kuma, ta umurci INEC da ta wallafa sunan Aro a matsayin halastaccen ɗan takarar APC a zaɓen majalisar dattawa na 2027.
Aro ya shigar da ƙarar ne domin kotu ta tabbatar da nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwani da aka gudanar ranar 18 ga watan Mayu.
Ya kuma nemi kotu ta soke miƙa sunan Karimi da APC ta yi wa INEC a matsayin ɗan takararta.
Lauyoyin Karimi da APC sun kalubalanci ƙarar
A yayin shari'ar, lauyoyin Karimi, INEC da APC sun nemi kotu ta yi watsi da ƙarar bisa hujjar cewa an shigar da ita ne bayan wa'adin da doka ta tanada.
Lauyan Karimi, John Olusola Baiyeshea, SAN, ya ce an gudanar da zaɓen fidda gwani ranar 18 ga Mayu, yayin da aka miƙa sunan Sanatan ga INEC ranar 29 ga Yuni.
Ya bayyana cewa Aro ya jira har zuwa ƙarshen watan Yuli kafin shigar da ƙarar, wanda ya ce ya saɓa wa tanadin sashe na 285 (9) na kundin tsarin mulkin Najeriya da ya tanadi kwanaki 14 domin shigar da irin waɗannan ƙorafe-ƙorafe.
Tsohon dan majalisa ya lashe zabe
Mun ba ku labarin cewa tsohon dan majalisar wakilai ya lashe zaben fitar da gwani na APC a mazabar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas da ke Plateau.
Dan siyasar ya samu kuri’u 12,181, yayin da babbar abokiyar hamayyarsa, Esther Simi Dusu, ta samu kuri’u 2,495 a zaben.
An gudanar da zaben ne bisa umarnin kotu bayan ta soke zaben farko saboda zargin kura-kurai a rumfunan zabe 11.
Asali: Legit.ng

