Sauki Zai Zo: Yadda Peter Obi Zai Saukar da Farashin Kayayyaki idan Ya Zama Shugaban Kasa
- Pat Utomi ya ce shirin tattalin arzikin NDC ƙarƙashin Peter Obi ya tanadi ƙarfafa Naira zuwa N500 kan dala
- Jam’iyyar ta yi hasashen cewa farashin buhun shinkafa zai sauka daga N55,000 zuwa N27,500, yayin da kwanon garri zai koma N650
- Utomi ya ce matakan za su taimaka wajen rage hauhawar farashi, talauci da tsadar rayuwa a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Farfesa Pat Utomi, masanin tattalin arziki kuma jigo a jam’iyyar NDC, ya bayyana cewa ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, na da shirin ƙarfafa darajar Naira zuwa N500 kan dala.
Utomi ya ce shirin zai kuma rage farashin kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki, inda kwanon garri zai sauka daga N1,300 zuwa N650.

Source: Facebook
Utomi yaa bayyana shirin karfafa darajar Naira
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Utomi ya ce NDC na da burin ganin an ƙarfafa darajar Naira daga kusan N1,350 zuwa N500 kan dala.
Ya bayyana cewa aiwatar da wannan manufa zai taimaka wajen rage tsadar rayuwa, musamman idan aka haɗa ta da zuba jari a fannin tsaro, wutar lantarki da hanyoyi.
Ya kuma ce shirin zai ƙunshi sauye-sauyen tsarin tattalin arziki da za su inganta gasa a kasuwanni, tare da rage matsin tattalin arzikin da jama’a ke fuskanta.
Jerin kayayyakin da NDC ke hasashen farashinsu zai sauka
Farfesan ya yi hasashen cewa idan aka cimma manufofin jam’iyyar, farashin wasu muhimman kayayyaki zai ragu sosai.
Ya bayar da misalan kayayyakin da farashinsu zai iya sauka kamar haka:
- Sinkin biredi zai sauka daga N1,750 zuwa N800.
- Buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 zai ragu daga N55,000 zuwa N27,500.
- Doya matsakaiciya za ta sauka daga N2,400 zuwa N1,200.
- Buhun masara mai kilo 50 zai ragu daga N75,000 zuwa N37,500.
- Kunshin ayaba zai sauka daga N2,500 zuwa N1,250.
- Kaza ɗaya za ta ragu daga N7,000 zuwa N3,500.
- Kwai guda 12 za su sauka daga N2,300 zuwa N1,150.
- Kwanon garri zai ragu daga N1,300 zuwa N650.
Utomi ya kuma lissafa fetur da siminti cikin kayayyakin da yake hasashen farashinsu zai ragu idan aka aiwatar da shirin tattalin arzikin jam’iyyar.
Abin da ya ce kan shirin rage tsadar rayuwa
Da yake ƙarin bayani kan manufar Naira, Utomi ya ce:
“Mun yi imanin cewa ƙudurin ƙarfafa darajar musayar kuɗi daga N1,350 kan dala zuwa N500, a matsayin wani ɓangare na manufofinmu, wata hanya ce da za ta taimaka wajen cimma burinmu.”
Ya ƙara da cewa shirin zai samar da hanyoyi daban-daban na rage hauhawar farashi, talauci da tsadar rayuwa.
A cewarsa, wannan mataki ya nuna ƙudurin jam’iyyar na inganta rayuwar ’yan Najeriya, musamman waɗanda ke fama da talauci ta fannoni daban-daban.

Source: Facebook
Peter Obi ya yi maganar rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaro.
Peter Obi ya danganta yawaitar rashin tsaro a Najeriya da matsanancin talauci, inda ya yi alkawarin yaki da fatara domin rage aikata laifuffuka idan aka zabe shi a 2027.
Asali: Legit.ng

