Duba Ta Cika: Mai Garkuwa da Mutane Ya Shiga Hannu Yana Kokarin Karbar Kudin Fansa
- An kama Mukaila Iliyasu a garin Akwaba da ke ƙaramar hukumar Eggon ta jihar Nasarawa, bisa zargin barazanar sace wata mata
- Wanda ake zargin ya nemi matar ta biya shi N200,000 domin kada ya sace ta, lamarin da ya kai ga haɗin gwiwar sojoji da DSS
- Jami’an tsaro sun kama shi ne yayin karɓar kuɗin, sannan suka miƙa shi ga DSS domin gudanar da bincike da yiwuwar gurfanar da shi a kotu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Nasarawa - Dakarun Sojojin Najeriya, tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), sun kama wani mutum da ake zargi da garkuwa da mutane yayin da yake ƙoƙarin karɓar kuɗin fansa a jihar Nasarawa.
An kama wanda ake zargin, mai suna Mukaila Iliyasu, a garin Akwaba da ke ƙaramar hukumar Eggon ta jihar, yayin wani samame na haɗin gwiwa tsakanin dakarun Sector 2 na rundunar haɗin gwiwa ta Operation Whirl Stroke da jami’an DSS.

Kara karanta wannan
Aminu Abdulsalam ya bayyana mutanen da yake zargi da yunkurin hana shi takara a Kano

Source: Original
Yadda wanda ake zargin ya nemi N200,000
Kamen ya biyo bayan samun bayanan sirri cewa Iliyasu ya yi barazanar sace wata mata idan ba ta biya shi kuɗin N200,000 ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Mukaddashin jami’in yaɗa labarai na Operation Whirl Stroke, Laftanar Ahmad Zubairu Zubairu, ne ya tabbatar da kamen a cikin wata sanarwa.
Sanarwar ta bayyana cewa jami’an DSS sun sanar da sojoji game da barazanar a ranar 29 ga Oktoba, lamarin da ya sa aka shirya wani samame na musamman domin gano wanda ake zargin da kuma hana sace matar.
Domin tabbatar da kama shi, wani soja ya shiga aikin basaja, inda ya yi kamar shi ne mutumin da aka tura domin kai kuɗin fansar.
An kama shi yayin karɓar kuɗin
Sanarwar ta ce jami’an tsaron sun yi nasarar cafke Iliyasu ne a daidai lokacin da yake karɓar kuɗin, inda suka ƙwato N200,000 da ake zargin kuɗin fansa ne da ya nema daga matar.
Rundunar sojin ta bayyana aikin a matsayin nasarar da aka samu ta hanyar bayanan sirri, wadda ta hana yiwuwar sace mutum.
Ta ce wannan nasara ta kuma nuna muhimmancin haɗin gwiwar hukumomin tsaro wajen yaƙi da ayyukan laifuffuka a faɗin ƙasar.
Bayan kama shi, an miƙa Iliyasu ga jami’an DSS domin ci gaba da gudanar da bincike da kuma yiwuwar gurfanar da shi a gaban kotu.
Kwamandan rundunar ya yaba wa jami’an tsaro
Kwamandan Operation Whirl Stroke kuma Babban Kwamandan runduna ta biyar ta Sojojin Najeriya, Manjo Janar Moses Kolo Gara, ya yaba wa sojoji da jami’an DSS bisa ƙwarewa, jarumtaka da kyakkyawar haɗin gwiwar da suka nuna.
Gara ya buƙaci jami’an tsaron da su ci gaba da aiki tare tare da ƙarfafa musayar bayanan sirri domin dakile garkuwa da mutane da sauran barazanar tsaro a yankunan da ke ƙarƙashin kulawarsu.
Ya kuma jaddada cewa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen kare rayukan jama’a, tabbatar da tsaron al’ummomi da kuma samar da zaman lafiya a yankin.

Source: Twitter
Sojoji sun kashe shugabannin ISWAP
A wani labarin kuma, kun ji cewa sojoji sun kashe manyan shugabannin ƙungiyar ISWAP guda huɗu, ciki har da Larabawa biyu da wani babban kwamanda, tare da wasu mayakan ƙungiyar.
Rundunar Sojojin Najeriya ta ce an kashe ’yan ta’addan ne a ranar 31 ga Oktoba, 2026, yayin wani samame da aka kai.
Asali: Legit.ng

