Shugaba Tinubu Ya Yi Wa kowane Dan Najeriya Addu'a a Ziyarar da Ya Kai Kasar Saudiyya
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kammala ziyarar ibada da ya je yi a kasar Saudiyya, inda ya yi wa Najeriya addu'a
- Bola Tinubu da tawagarsa sun samu damar shiga cikin Ka’aba mai alfarma a Makka domin yin addu’a da Umrah a yayin ziyarar
- Ya gode wa Sarkin Saudiyya da yarima mai jiran gado bisa damar da suka ba su da kyakkyawar tarbar da suka yi musu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da kammala ziyarar da ya kai kasar Saudiyya domin yin ibada da addu'o'i ga Najeriya.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce ya yi addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da wadata ga Najeriya da al’ummarta a yayin ziyarar da ya kai Masarautar Saudiyya.

Source: Facebook
Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a ranar Litinin, wadda ya wallafa a shafinsa na X da aka tantance bayan kammala ziyararsa a ƙasa mai tsarki.

Kara karanta wannan
Tsohon sanata kirista ya kalubalanci Shugaba Tinubu ya zo su yi gasar karatun Kur'ani
Shugaban ƙasar ya ce shi da mambobin tawagarsa sun samu wata dama ta musamman ta shiga cikin Ka’aba mai alfarma da ke Makka domin yin addu’a da gudanar da ibadar Umrah.
Tinubu ya yi wa yan Najeriya addu'a
Tinubu ya bayyana cewa ya yi wa kasa addu'a, sannan ya yi wa kowane dan Najeriya addu'a a tsawon lokacin da ya shafe a kasa mai tsarki.
Ya bayyana cewa sun yi amfani da wannan dama wajen gabatar da addu’o’i tare da gudanar da ibadar Umrah.
Shugaban ƙasar ya bayyana lokacin a matsayin na musamman, inda ya yi addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da wadata ga Najeriya da al’ummarta.
Tinubu ya ce addu’ar ta shafi ƙasar baki ɗaya da kuma dukkan ’yan Najeriya, ba tare da ware wani ɓangare na al’ummar ƙasar ba.
Tinubu ya gode wa jagororin Saudiyya
Ya nuna godiyarsa ga Sarkin Saudiyya da mai kula da manyan masallatai biyu masu alfarma, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud.
Ya kuma gode wa Yarima Mai Jiran Gado kuma Firaministan Saudiyya, Mohammed bin Salman, bisa ba su wannan dama da kuma kyakkyawar tarbar da suka yi wa tawagar Najeriya.

Source: Facebook
Tinubu ya ce wannan karamci ya nuna irin dadaddiyar alaƙar addini da zumuncin da ke tsakanin Najeriya da Saudiyya.
“A cikin waɗannan lokuta masu alfarma, na yi addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da wadata ga ƙasarmu da kuma dukkan ’yan Najeriya,” in ji Tinubu.
Tinubu ya taya Sarkin Musulmi murna
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, murnar cika shekaru 20 a kan karagar mulki.
Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin sakon taya murna da ya aika wa Sarkin Musulmin, inda ya yaba da yadda ya jagoranci masarautar cikin shekarun da suka gabata.
Asali: Legit.ng
