Shugaba Tinubu Ya Saduda, Ya Bayyana Wanda Zai Iya Kwace Mulki a Hannunsa

Shugaba Tinubu Ya Saduda, Ya Bayyana Wanda Zai Iya Kwace Mulki a Hannunsa

  • Tinubu ya ce Allah na iya karɓe mulki daga hannunsa ya ba wani idan bai yi amfani da shi bisa umarninSa ba
  • Shugaban ya bayyana cewa ya roƙi Allah ya ba shi hikima da juriyar ci gaba da yi wa ’yan Najeriya hidima
  • Tinubu ya ce tattalin arzikin Najeriya ya fito daga wani mawuyacin hali, sannan ya jaddada buƙatar zuba jari a makomar matasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Makkah, Saudiyya - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Allah ne ke bayar da mulki kuma yake karɓe shi.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Allah zai iya karɓe mulkin daga hannunsa ya ba wani idan bai yi amfani da shi bisa umarninSa ba.

Tinubu ya yi magana kan mulki
Shugaba Bola Tinubu a wajen taron APC a Kaduna Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta bidiyo da shafin fadar shugaban kasar Najeriya ya wallafa a X ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamban 2026.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Tinubu ya fada kan zabe bayan shiga dakin Ka'aba a Saudi

Shugaban ya ce ya roƙi Allah ya ba shi hikima da juriyar ci gaba da yi wa ’yan Najeriya hidima a lokacin ziyarar ibadar da ya kai birnin Makka da ke Saudiyya a baya-bayan nan.

Tinubu ya mika lamarinsa ga Allah

A cikin hirar, Tinubu ya bayyana cewa Allah ne ke da cikakken iko a kan mulki, kuma shi ne ke ba da shi ko kuma ya karɓe shi daga hannun duk wanda yake riƙe da shi.

Ya ce Allah yana buƙatar shugabanni su yi amfani da ikon da aka ba su yadda ya kamata, bisa ƙa’idojin da Ya gindaya.

A kalamansa:

“Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah Maɗaukakin Sarki. Shi ne mai bayarwa kuma mai karɓewa. Shi ne mamallakin iko. Yana cewa a yi amfani da shi yadda ya kamata. Idan ba ka yi amfani da shi bisa umarnina ba, zan iya karɓe shi daga gare ka in ba wani.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi Umrah a Saudiyya, ya bayyana addu'o'in da ya yi wa Najeriya

Shugaban ya ƙara da cewa ganin yadda Najeriya take da miliyoyin mutane, zama shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunar sojojin ƙasar wata ni’ima ce daga Allah.

Ya ce samun wannan matsayi a tsakanin dimbin al’ummar ƙasar wata babbar falala ce da ya kamata mutum ya gode wa Allah a kanta.

Me Tinubu ya ce kan tattalin arziki?

Shugaban ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da aiwatar da manufofin da za su kawo ci gaba da wadata a Najeriya, bisa amannarsa da kuma burin ’yan ƙasar.

Dangane da tattalin arziki, Tinubu ya nuna kyakkyawan fata kan halin da ƙasar ke ciki, yana mai cewa an kafa tubali mai ƙarfi kuma tattalin arzikin ya fito daga wani mawuyacin hali.

Ya bayyana cewa wannan ci gaba yana ƙarfafa gwiwa, duk da cewa akwai buƙatar ci gaba da yin aiki domin tabbatar da dorewar nasarorin da aka samu.

Tinubu ya yi addua ga Najeriya
Shugaba Bola Tinubu a wajen Umrah a Saudiyya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Atiku ya fadi kuskuren Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ​dan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya caccaki kwamitin yaƙin neman zaɓen APC da Bola Tinubu.

Atiku ya zargi kwamitin da ƙoƙarin ɓoye gazawar Shugaba Bola Tinubu wajen cika alkawarin samar da wutar lantarki mai ɗorewa, ta hanyar jerin dokoki da ayyuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng