Gwamnan da ke Goyon Bayan Tinubu a 2027 Ya Watsa Wa APC Kasa a Ido

Gwamnan da ke Goyon Bayan Tinubu a 2027 Ya Watsa Wa APC Kasa a Ido

  • Adeleke ya musanta cewa ya yi yarjejeniya da APC kan rabon kujerun majalisa da shugabancin ƙananan hukumomi a Osun
  • Gwamnan ya ce haɗin gwiwarsa da fadar shugaban ƙasa na da alaƙa ne kawai da sake zaɓen Bola Tinubu a 2027
  • Ya tabbatar da cewa zai goyi bayan ’yan takarar jam’iyyar Accord a zaɓen majalisar dattawa, wakilai da majalisar dokokin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Osun - Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa akwai yarjejeniya tsakaninsa da jam'iyyar APC.

Gwamna Adeleke ya musanta rahotannin da ke cewa ya cimma yarjejeniya da jam’iyyar APC domin raba kujerun majalisa da muƙaman ƙananan hukumomi a jihar gabanin babban zaɓen 2027.

Adeleke ya musanta yarjejeniya da APC
Gwamna Ademola Adeleke tare da Shugaba Bola Tinubu Hoto: @AAdeleke01
Source: Twitter

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, Mallam Olawale Rasheed, inda ya ce rahotannin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta ƙirƙirarru ne, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kawar da shakkun 'yan Najeriya, ya fadi dalilinsa na runtumo basussuka

Ya jaddada cewa fahimtar siyasar da ke tsakaninsa da fadar shugaban ƙasa ba ta ƙunshi wata yarjejeniya ta raba muƙaman zaɓe da APC a Jihar Osun ba.

Adeleke ya ce zai goyi bayan Tinubu

Adeleke ya sake tabbatar da goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027.

Sai dai ya bayyana cewa manufar haɗin gwiwar siyasar ita ce taimaka wa Tinubu ya samu wa’adi na biyu, ba wai ƙulla yarjejeniya kan sakamakon sauran zaɓukan da za a gudanar ba.

Gwamnan ya ce ya kamata a fahimci cewa jam’iyyun da ke cikin haɗin gwiwar suna da ’yancin fafatawa da juna a sauran zaɓuka, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Jam’iyyar Accord za ta fafata a zaɓen majalisa

Adeleke ya bayyana cewa ’yan takarar jam’iyyar Accord, wadda ya yi takara a ƙarƙashinta a zaɓen gwamnan Osun na ranar 15 ga Agustan 2026, za su fafata a dukkan zaɓukan majalisa.

Kara karanta wannan

Tafiyar Tinubu zuwa Makkah ta jawo masa abin da bai yi zato ba

Ya ce ’yan takarar jam’iyyar za su shiga zaɓen kujerun majalisar dattawa, majalisar wakilai da kuma majalisar dokokin Jihar Osun.

Gwamnan ya jaddada cewa masu zaɓe ne za su yanke hukuncin waɗanda za su lashe kujerun, yayin da kowace jam’iyya ke da ’yancin tsayar da ’yan takara da yi musu kamfen.

Ya kuma ce da kansa zai fito ya goyi bayan ’yan takarar Accord da ke neman kujeru a Majalisar Tarayya da majalisar dokokin jihar.

Ya yi watsi da zargin raba muƙamai

Adeleke ya ce babu wata yarjejeniya da za ta tilasta wa jam’iyyar Accord yin watsi da muradunta na siyasa domin bai wa APC damar samun kujeru.

Ya ƙara da cewa yarjejeniyar da ke tsakanin abokan haɗin gwiwar siyasar ta tsaya ne kan zaɓen shugaban ƙasa, yayin da kowace jam’iyya za ta ci gaba da neman nasara a sauran zaɓuka.

Wannan ƙarin bayani na gwamnan ya biyo bayan rahotannin da ke cewa dangantakarsa da fadar shugaban ƙasa ta ƙunshi wata yarjejeniya mai faɗi, wadda za ta bai wa APC da Accord damar raba kujerun majalisa da muƙaman ƙananan hukumomi a Osun.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu na shirin sanya INEC dage zaben 2027? An ji yadda zancen yake

Sai dai Adeleke ya yi watsi da wannan batu, yana mai cewa jam’iyyarsa za ta ci gaba da fafatawa domin samun nasara a zaɓukan da ke tafe.

Adeleke ya musanta yarjejeniya da APC
Gwamna Ademola Adeleke na jawabi a wajen taro Hoto: Pelumi Olajangbesi
Source: Facebook

Adeleke ya yaba wa Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bayan sake zabensa a matsayin gwamnan jihar a zaben da aka gudanar ranar 15 ga Agusta.

Gwamnan ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya kira shi domin taya shi murnar nasarar da ya samu a zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng