ADC na Neman Darewa Saboda Takarar Atiku a 2027? An Ji Yadda Lamarin Yake
- Shugabannin ADC a Kudu maso Yamma sun yi magana kan batun rikici ko rarrabuwar kawuna a tsakaninsu
- Jam’iyyar ta ce taron da aka gudanar a Ibadan ranar 4 ga Satumba, 2026, an shirya shi ne domin ƙarfafa tsarin jam’iyyar da dabarun cin zaɓe
- ADC ta musanta zargin cewa an gudanar da taron tattaunawa ta intanet da Atiku ranar 5 ga Satumba domin sasanta rikicin cikin gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Oyo - Shugabancin jam’iyyar ADC na shiyyar Kudu maso Yamma ya sake tabbatar da haɗin kai da goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, da sauran ’yan takararta a zaɓen 2027.
A wata sanarwa da mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa mai kula da shiyyar Kudu maso Yamma, Akin Omole, da shugabannin ADC na jihohi shida suka sanya wa hannu, jam’iyyar ta musanta samun rikici ko rabuwar kai a cikinta.

Kara karanta wannan
An fara batun Tinubu ya je Umrah ne don neman kuri'un 'yan Arewa, hadiminsa ya magantu

Source: Facebook
Sanarwar ta bayyana cewa shugabancin shiyyar da shugabannin jihohin shida suna tare da manufa guda, kuma sun ƙuduri aniyar ƙarfafa tsarin jam’iyyar a faɗin yankin, cewar rahoton jaridar Leadership.
ADC ta tabbatar da goyon bayanta ga Atiku
A cikin sanarwar, shugabannin jam’iyyar sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Atiku Abubakar, tare da yabawa da ƙwarewarsa ta siyasa da hangen nesansa na tafiyar da ƙasa.
Sun ce suna da niyyar yin aiki kafada da kafada da shi, kwamitin gudanawar na kasa (NWC), shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata David Mark, da sakataren jam’iyyar, Ogbeni Rauf Aregbesola, domin samun gagarumar nasara a 2027.
Sun kuma sake jaddada amincewarsu da jagoranci da dabarun tafiyar da harkokin siyasa na Aregbesola a faɗin Kudu maso Yamma.
Jam’iyyar ta bayyana dalilin taron Ibadan
Shugabannin ADC sun ce taron da aka gudanar a Ibadan ranar 4 ga Satumba, 2026, taro ne na dabarun siyasa da aka shirya domin tattauna hanyoyin ƙarfafa jam’iyyar a yankin.
Sun bayyana cewa an mayar da hankali kan tsara dabarun siyasa, wayar da kan jama’a a matakin ƙasa da ƙasa, hulɗa da masu ruwa da tsaki da kuma daidaita ayyukan jam’iyyar.
A cewarsu, taron bai kasance wani yunƙuri na adawa da Atiku, shugabancin jam’iyyar na ƙasa ko wani mutum a cikinta ba, jaridar The Punch ta kawo labarin.
ADC ta musanta batun taron sulhu da Atiku
Sanarwar ta kuma musanta cewa an gudanar da taron tattaunawa ta intanet da Atiku Abubakar ranar 5 ga Satumba, 2026.
Shugabannin sun ce duk wani iƙirarin cewa an gudanar da irin wannan taro domin sasanta rikicin cikin gida ƙarya ne da aka ƙirƙira.
Sun zargi abokan hamayyarsu na siyasa da ƙoƙarin haddasa rashin jituwa da raunana haɗin kan da jam’iyyar ke ƙoƙarin ginawa.
Sun buƙaci mambobi da magoya bayan ADC da su yi watsi da labaran da za su iya haifar da rarrabuwar kawuna a cikinsu.
Sun ƙara da cewa babu rashin jituwa, gaba ko rabuwar kai tsakanin shugabancin ADC na Kudu maso Yamma da ɗan takarar shugaban ƙasarta.
A ƙarshe, shugabannin sun jaddada cewa jam’iyyar a shirye take ta haɗa kai domin ganin Atiku Abubakar da sauran ’yan takarar ADC sun samu nasara a yankin Kudu maso Yamma a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Aminu Abdulsalam ya bayyana mutanen da yake zargi da yunkurin hana shi takara a Kano

Source: Facebook
Hadimin Atiku ya soki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Phrank Shaibu, ya ce ibadar Umrah da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai ƙasar Saudiyya ba za ta ba shi tabbacin tazarce ba ba.
Phrank Shaibu, wanda ke magana a madadin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa samun wa'adin mulki na biyu ba ya dogara da ikirarin ibada ko addu'o'in da mutum ya yi.
Asali: Legit.ng
