Hadimin Atiku Ya Zargi Tinubu da Siyasantar da zuwa Umrah Saudi

Hadimin Atiku Ya Zargi Tinubu da Siyasantar da zuwa Umrah Saudi

  • Daraktan yaɗa labarai na kwamitin kamfen na ADC, Phrank Shaibu, ya ce ziyarar ibadar Umrah da Bola Tinubu ya kai Saudiyya ba za ta tabbatar masa da nasara a zaɓen 2027 ba
  • Shaibu ya soki yadda magoya bayan shugaban ƙasar ke siyasantar da ziyarar ibadar, yana mai cewa ba za a samu wa'adin mulki na biyu ta hanyar ikirarin ibada ba
  • Ya kuma soki gwamnatin Tinubu kan halin matsin tattalin arzikin da 'yan Najeriya ke ciki, yana mai cewa jama'a za su tuna da addu'o'in da shugaban ya yi a Makka tare da tsadar rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC, Phrank Shaibu, ya ce ibadar Umrah da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai ƙasar Saudiyya ba za ta ba shi tabbacin tazarce ba ba.

Kara karanta wannan

An fara batun Tinubu ya je Umrah ne don neman kuri'un 'yan Arewa, hadiminsa ya magantu

Shaibu, wanda ke magana a madadin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa samun wa'adin mulki na biyu ba ya dogara da ikirarin ibada ko addu'o'in da mutum ya yi.

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Atiku Abubakar a hagu da Bola Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Atiku Abubakar
Source: Facebook

Shaibu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.

Abin da ADC ta ce kan ziyarar Tinubu

Shaibu ya ce ziyartar ƙasa mai tsarki domin gudanar da ibada abu ne na mutum da kansa, ba wai abin da ya kamata a mayar da shi wani taron siyasa ba.

Ya zargi magoya bayan Tinubu da amfani da ziyarar ibadar domin cimma muradun siyasa, yana mai tambayar sahihancin yadda ake nuna addinin shugaban ƙasar.

Ya kuma yi ikirarin cewa da gaske Tinubu yana aiwatar da abin da yake ikirarin yi na addini, da ba a ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ba.

Sai dai Shaibu bai bayyana wata hujja da ta tabbatar da alaƙar da ya yi tsakanin batun tsare El-Rufai da ibadar shugaban ƙasar ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi wa kowane ɗan Najeriya addu'a a ziyarar da ya kai ƙasar Saudiyya

Hadimin Atiku ya soki Tinubu

Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC ya kuma soki Tinubu kan yadda ya yi magana a Saudiyya, a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke fama da matsin tattalin arziki.

The Cable ta rahoto cewa ya yi watsi da ikirarin gwamnatin cewa tattalin arzikin ƙasar na samun ci gaba, yana mai cewa har yanzu al'umma na fuskantar tsadar abinci, kayayyaki da saurasu.

A cewarsa, 'yan Najeriya za su tuna da addu'o'in da shugaban ƙasar ya yi a Makka tare da irin tsadar rayuwar da suke fuskanta a gida.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Lokacin da shugaba Bola Tinubu zai shiga Ka'aba. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Da aka tambaye shi ko Atiku Abubakar zai raka Tinubu Saudiyya idan an gayyace shi, Shaibu ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar ne ya ɗauki nauyin tafiyar Tinubu ta farko zuwa Makka.

Ya kuma nuna kwarin gwiwa kan damar Atiku na samun goyon baya a jihohin Arewa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar yana da kyakkyawar damar samun nasara a yankin.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Tinubu ya fada kan zabe bayan shiga dakin Ka'aba a Saudi

Tinubu ya shiga Ka'aba

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da yi wa Najeriya hidima da kuma gina ƙasa mai wadata bayan samun damar shiga cikin Ka'aba a Makka.

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ya roƙi Allah Ya ba shi hikima da ƙarfin jure ƙalubale domin ci gaba da jagorantar 'yan Najeriya.

Shugaban ƙasar ya kuma ce aniyarsa ta gina Najeriya da samar da kyakkyawar makoma ga matasa ta ƙara ƙarfi bayan wannan tafiya ta ibada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng