An Dauki Bidiyon Wani Malami Yana Rera Wakar Goyon Bayan Peter Obi da Kwankwaso
- Limamin wata coci ya jagoranci mabiya cocinsa wajen rera waƙar yabon jam’iyyar NDC a lokacin ibada ranar Lahadi da ta gabata
- Waƙar ta bayyana jam’iyyar NDC da tikitin takarar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a matsayin dandalin da ya fi dacewa da yan Najeriya
- Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da wasu shugabannin addini ke bayyana goyon bayansu ga ’yan takarar shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abia, Nigeria - An ɗauki bidiyon wani limamin cocin Katolika yana rera waƙar yabon Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC da abokin takararsa, Rabiu Musa Kwankwaso, a lokacin ibadar ranar Lahadi.
Waƙar ta bayyana NDC a matsayin jam’iyyar siyasa da ta fi dacewa da yan Najeriya a daidai wannan lokaci da kasar ke fuskantar kalubale.

Kara karanta wannan
Aminu Abdulsalam ya bayyana mutanen da yake zargi da yunkurin hana shi takara a Kano

Source: Facebook
A cikin wani bidiyo da ya yaɗu a shafin X wanda aka wallafa a shafin Precious Oruche, an ga limamin yana jagorantar mabiya cocin wajen rera waƙa da harshen Igbo, inda wasu daga cikin masu ibadar suka bi shi.
“Jam’iyyar Peter Obi ta fi kyau; jam’iyyar Kwankwaso ta fi kyau!” in ji limamin yayin da yake rera waƙar.
Malaman addini na faɗar ra’ayoyinsu
Yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa, shugabanni da malaman addinai na ƙara bayyana ra’ayoyinsu kan ’yan takarar siyasa, inda wasu ke sukar wasu ’yan takara a fili, yayin da wasu kuma ke bayyana goyon bayansu gare su.
A watan Agusta, an ruwaito cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya bukaci Musulmi su zaɓi tikitin Musulmi da Musulmi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Da yake magana a wani bikin ɗaurin aure na ma’aurata 1,500 da gwamnatin jihar Kano ta shirya, Jingir ya bukaci Musulmi su yi zaɓe ta hanyar da za ta nuna irin ƙarfin yawansu a ƙasar.
Kwankwaso ya yi Allah wadai da kalaman Jingir a wani saƙo da ya wallafa a shafin X.
Ƙungiyar bishop ta goyi bayan Tinubu
Haka kuma, Ƙungiyar Bishof-bishof Ta Najeriya (CBCN) ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sake tsayawa takara karo na biyu.
Bishof-bishof ɗin sun bayyana matsayinsu ne a taron majalisar ƙungiyar na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja, babban birnin ƙasar.

Source: Facebook
Taron ya samu halartar George Akume, sakataren gwamnatin tarayya (SGF), da Mohammed Idris, ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a.
Wakilan CBCN daga shiyyoyin siyasa shida na ƙasar sun buƙaci shugaban ƙungiyar na ƙasa, Leonard Kawas, da ya sanar da matsayar taron.
Peter Obi ya yi alkawarin shiga daji
Kun ji cewa Peter Obi ya sha alwashin shiga dazuzzuka domin ceto wadanda aka sace idan aka zabe shi shugaban kasa a zaben 2027.
Dan takarar shugaban kasa na NDC ya ce gwamnatinsa za ta magance matsalar garkuwa da mutane, tare da tabbatar da tsaron hanyoyin Najeriya.
Asali: Legit.ng
