Takarar Makinde Ta Fara Tangal Tangal, Masu Muƙamai 3 Su Yi Murabus

Takarar Makinde Ta Fara Tangal Tangal, Masu Muƙamai 3 Su Yi Murabus

  • Kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki na Oyo, Ayobami Ojo, da wasu manyan hadiman Gwamna Seyi Makinde biyu sun yi murabus
  • Adegbola Oyeleke ya bayyana cewa ba ya jin daɗin yanayin aikin gwamnatin, wanda ya hana shi cimma muradun al'ummar da yake wakilta
  • Murabus ɗin na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen zaɓen gwamnan Oyo na 2027 da zaɓen ƙananan hukumomi 33 a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Manyan jami'ai uku da ke aiki a gwamnatin Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo sun yi murabus daga muƙamansu a ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba, 2026.

Jami'an sun haɗa da Kwamishinan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Ayobami Ojo; mai ba gwamna shawara na musamman kan kasafin kuɗi, Adegbola Oyeleke; da mamban hukumar zaɓen jihar, Sunday Falana.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya nada sababbin kwamishinoni, mai magana da yawunsa ya samu babban mukami

Muƙarraban gwamnatin Makinde 3 sun yi murabus
Dan takarar shugaban kasa a APM, Seyi Makinde da mataimakinsa, Lawal Daura. Hoto: Seyi Makinde.
Source: Facebook

Wadanda suka yi murabus a gwamnatin Makinde

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a watan Oktoba, shugaban ma'aikatan gwamnan, Segun Ogunwuyi, shi ma ya yi murabus bayan shafe sama da shekaru biyar yana aiki.

Ojo, wanda ya fito daga garin Ago-Are da ke ƙaramar hukumar Atisbo a jihar, ya aika da takardar murabus ɗinsa ga gwamnan ta hannun Sakataren Gwamnatin Jiha, Farfesa Musibau Babatunde.

Bayan murabus ɗinsa, tsohon darakta janar na ofishin kula da ayyukan kwangiloli na jihar, Tara Adefope, shi ma ya ajiye aikinsa.

Ogunwuyi, wanda ya taɓa zama ɗan majalisar wakilai ta tarayya, bai bayyana dalilin barin muƙaminsa a bainar jama'a ba.

Dalilan da suka sa jami'an suka yi murabus

Sai dai Ojo ya ambaci wasiƙar naɗinsa mai ɗauke da ranar 22 ga watan Yuni, 2026, inda ya bayyana cewa murabus ɗinsa zai fara aiki nan take.

Kwamishinan bai bayyana dalilin barin majalisar zartarwar jihar ba, amma ya gode wa Gwamna Makinde bisa amincewar da ya nuna masa da kuma damar da ya ba shi na yi wa jihar hidima.

Kara karanta wannan

"Ba sabon alkawari ba"; Gwamna Radda ya fadi abin da yake kamfen da shi

Haka kuma, Oyeleke, wanda ya taɓa zama ɗan majalisar dokokin jihar na wa'adi biyu kuma shugaban ƙaramar hukuma, ya sanar da murabus ɗinsa a matsayin mai ba gwamna shawara na musamman kan kasafin kuɗi.

A wasiƙarsa mai ɗauke da ranar 2 ga watan Nuwamba, 2026, wadda ya aikewa Makinde kai tsaye, Oyeleke ya ce ba ya jin daɗin yanayin aiki a cikin gwamnatin

Makinde ya rasa mukarraban gwamnatinsa 3
Dan takarar shugaban kasa a APM, Seyi Makinde. Hoto: Seyi Makinde.
Source: Facebook

Sauran wadanda suka yi murabus

Jami'i na uku, Falana, wanda ya fito daga Ogbomoso, shi ma ya yi murabus daga muƙaminsa na mamba a hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Oyo (OYSIEC).

A wasiƙarsa mai ɗauke da ranar 2 ga watan Nuwamba, wadda ya aika wa gwamnan ta hannun shugaban ma'aikatansa, Falana ya ce murabus ɗinsa zai fara aiki nan take.

Bai bayyana dalilin yanke shawarar barin muƙaminsa ba, amma ya gode wa Seyi Makinde bisa damar da ya ba shi na aiki a hukumar gudanar da zaɓukan jihar, yana mai bayyana lokacin da ya shafe a matsayin mai amfani.

APM ta magantu kan murabus ɗin jami'an

Da aka tuntuɓi Darakta Janar kan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na kwamitin yaƙin neman zaɓen Bimbo Adekanmbi, Yinka Oladoyinbo, ya ce murabus ɗin ba zai shafi damar ɗan takararsu na APM ba a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

An yi rashi: Basarake kuma babban malamin addini ya yi bankwana da duniya

Ya ce zaɓen ba na 'yan siyasa kaɗai ba ne, domin al'ummar Oyo miliyan 7.9 ne za su yanke shawarar wanda zai zama gwamnan jihar.

Tinubu ya gaza a mulki - APM

An ji cewa kungiyar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta Makinde-Daura (MDPCO) ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye takararsa ta neman wa'adi na biyu a zaɓen 2027.

Kungiyar ta ce Najeriya na buƙatar shugaban ƙasa mai ƙarfi da kuzarin jagorantar ƙasar, tana mai zargin cewa Tinubu ba shi da ƙarfin da ake buƙata domin ci gaba da gudanar da mulki.

Ta kuma yi kira ga 'yan Najeriya su sabunta katin zaɓensu tare da kaɗa ƙuri'a domin kayar da Tinubu idan bai saurari shawarar da ta ba shi na janye takararsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.