An Tura Ƙalubale kan lafiyar Tinubu, Atiku da Zai Iya Jawo Masu Matsala a Zaɓe

An Tura Ƙalubale kan lafiyar Tinubu, Atiku da Zai Iya Jawo Masu Matsala a Zaɓe

  • Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya yi tsalle daga kan dandamali a Ondo, inda ya ƙalubalanci sauran ’yan takarar shugaban ƙasa su nuna ƙarfinsu
  • Makinde ya ce bai damu da shekarun ’yan takara ba, sai dai kuzari da ƙarfin da za su iya gudanar da ayyukan shugaban ƙasa
  • Ya kuma kare takararsa ta shugaban ƙasa duk da cewa Bola Tinubu, ɗan Kudu maso Yamma, na neman wa’adin mulki na biyu a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya ƙalubalanci sauran takarar shugaban kasa a Najeriya.

Makinde ya bukaci’yan Najeriya da su yi la’akari da kuzari da ƙarfin ’yan takarar da ke neman shugabancin ƙasa a zaɓen 2027.

Makinde ya kalubakanci Atiku da Tinubu
Dan takarar shugaban kasa a APM, Seyi Makinde. Hoto: Seyi Makinde.
Source: Facebook

Makinde ya kalubalanci takarar Atiku da Tinubu

Makinde, wanda yake takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), ya yi wannan ƙalubale ne a ranar Alhamis, yayin taron tattaunawa da jama’a na yankin Kudu maso Yamma, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Makinde ya faɗi dalilin ƙalubakantar Tinubu duk da sun fito daga yanki ɗaya

An gudanar da taron ne a Akure, babban birnin jihar Ondo, ƙarƙashin ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Makinde/Daura domin neman goyon bayan jama'a a zaben shekarar 2027.

Gwamnan ya ce ba zai mayar da shekarun ’yan takara muhimmiyar magana ba a zaɓen shugaban ƙasa, sai dai zai fi mayar da hankali kan ƙarfinsu da kuma yadda za su iya jure nauyin aikin shugabancin ƙasa.

Domin tabbatar da abin da yake faɗa, Makinde ya yi tsalle daga kan dandamalin da yake magana, sannan ya ƙalubalanci sauran ’yan takarar shugaban ƙasa da su yi irin haka.

Ya ce:

“Idan suka kawo ɗan takararsu na shugaban ƙasa, a bar shi ya zo nan shi ma ya yi tsalle daga kan dandamali, idan za su iya yin haka, ku zaɓe su.”
Makinde ya yi ba'a ga Atiku, Tinubu
Dan takarar shugaban kasa a APM, Seyi Makinde. Hoto: Seyi Makinde.
Source: UGC

Makinde ya soki gwamnatin Tinubu

Makinde ya buƙaci al’ummar yankin Kudu maso Yamma da su ƙi abin da ya kira siyasar yaudara, sannan ya zargi gwamnatin Tinubu da almubazzaranci da kuɗaɗen masu biyan haraji.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci sun gargaɗi ’yan Najeriya kan sayar da ƙuri’a a zaben 2027

Ya kuma soki Jimoh Ibrahim, wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, kan tafiyar da ya yi daga New York zuwa Abuja domin miƙa kasafin kuɗin Majalisar Ɗinkin Duniya ga Tinubu.

Gwamna Makinde ya tambayi dalilin wannan tafiya, yana mai cewa gwamnatin tarayya ba ta bayyana wa ’yan Najeriya takamaiman kasafin kuɗin da take amfani da shi ba.

Makinde ya kare takararsa duk da takarar Tinubu

An ji cewa Gwamna Seyi Makinde ya kare matakin da ya ɗauka na tsayawa takarar shugaban ƙasa, duk da cewa Shugaba Bola Tinubu na yankinsa.

Makinde ya ce ya ji wasu mutane suna tambayar dalilin da ya sa yake takara alhali yankin Kudu maso Yamma yana da wanda yake kan kujerar shugaban ƙasa.

Ya ce ya bayyana musu cewa akwai misali a tarihin siyasar yankin da ke nuna cewa babu laifi ’yan takara biyu daga yanki ɗaya su fafata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.