An Tura Jarumar Fim Kurkuku kan Zargin Fitar da Hoton Tsiraici

An Tura Jarumar Fim Kurkuku kan Zargin Fitar da Hoton Tsiraici

  • Wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta bayar da umarnin tsare jaruma Doris Ogala a gidan gyaran hali na Kirikiri kan zargin cin zarafin fasto Chris Okafor
  • Ana zarge ta da wallafa hotunan sirri na faston ba tare da izininsa ba, yaɗa saƙonni da ake zargin ƙarya ne, da kuma yi masa barazanar ci gaba da wallafa bayanan shi
  • Alƙali Akintayo Aluko ya ɗage shari’ar zuwa 30 ga Oktoba, 2026, domin sauraron buƙatar belin jarumar, inda ya umarci a ci gaba da tsare ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas – Wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta bayar da umarnin tsare jarumar fina-finan Najeriya, Doris Ogala, a gidan gyaran hali na Kirikiri.

An tura ta kurkuku ne yayin da ake jiran sauraron buƙatarta ta belin kan zargin cin zarafi ta intanet da yunƙurin karɓar kuɗi ta hanyar barazana ga Fasto Chris Okafor.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga suka kafa gwamnatinsu, suke karɓar haraji kala 3 a jihohin Arewa 2

Jaruma Doris Ogala
Jaruma Doris Ogala da aka tura kurkuku. Hoto: Doris Ogala
Source: Instagram

Punch ta wallafa cewa an gurfanar da jarumar ne a gaban Mai Shari’a Akintayo Aluko bisa tuhume-tuhume guda uku da ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya ya shigar a kanta.

Zargin da aka yi wa jarumar

Lauyan masu gabatar da ƙara, Tolulope Mokolu, ya shaida wa kotun cewa ana zargin Ogala da aikata laifuffukan tsakanin Satumban 2024 da Maris 2026.

Mokolu ya yi zargin cewa jarumar ta wallafa hotunan tsiraici da na sirri na Fasto Okafor a shafukanta na sada zumunta ba tare da izininsa ba.

A cewar mai gabatar da ƙarar, wallafa hotunan na iya jawo wa faston abin kunya, damuwa da kuma ɓata masa suna. Ya ƙara da cewa daga baya an yaɗa hotunan a wasu shafukan yanar gizo da kafafen sada zumunta.

Sai dai waɗannan zarge-zarge ne da ake gabatarwa a kotu, kuma jarumar ta musanta dukkan tuhume-tuhumen da aka karanta mata.

Ana zargin ta da neman kudi

Kara karanta wannan

Matasa sun kira sarki a waya, sun yi barazanar yin garkuwa da shi a Kano

Mai gabatar da ƙarar ya kuma zargi Ogala da wallafa bidiyoyi, na’urorin sauti da saƙonnin lantarki da ake zargin ta san ƙarya ne, da nufin tsoratarwa, cin zarafi da kuma tursasa faston.

Mokolu ya ce ana zargin jarumar ta aika saƙonnin da ke barazanar ci gaba da wallafa bayanan sirri da abubuwan da za su tsoratar da Okafor, matuƙar bai biya ta diyya ba ko kuma ya saya mata gida.

A cewar lauyan, ana zargin ta yi hakan ne domin ɓata sunan faston da kuma jefa shi cikin abin kunya a idon jama’a.

Dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore ya yi Allah wadai da tura jarumar kurkuku a wani sako da ya wallafa a Facebook.

Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore
Omoyele Sowore da ya yi adawa da kulle jaruma Doris. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Getty Images

Kotu ta ci tarar INEC

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta soke matakin INEC na wallafa sunan Ibrahim Lukman a matsayin ɗan takarar jam’iyyar NDC mai neman kujerar majalisar wakilai ta Oshodi/Isolo I a zaɓen 2027.

Mai Shari’a Akintayo Aluko ya yanke hukuncin ne a ranar 20 ga Oktoba, 2026, bayan kotun ta gano cewa Lukman bai shiga zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar da aka gudanar a ranar 29 ga Mayu ba.

Kotun ta umarci INEC da ta wallafa sunan Owadara da bayanansa a matsayin ɗan takarar jam’iyyar, tare da umartar hukumar da Lukman su biya kuɗin shari’a na Naira miliyan ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng