"Abin da Muke Gani Ya Karfafa Mana Gwiwa"; Radda Ya Nemi a Goyi bayan Tinubu da APC
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa ya gamsu da abubuwan da ya gani a Danja
- Malam Dikko Umaru Radda ya jaddada aniyarsa na ci gaba da samar da ayyukan da za su inganta rayuwar al'umma
- Gwamnan na Katsina ya lissafo nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannonin ilmi, noma, kiwon lafiya da tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana gamsuwarsa da yadda goyon bayan al’ummar Ƙaramar Hukumar Danja ga Jam’iyyar APC ke ƙaruwa.
Gwamna Radda ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da samar da ayyukan raya ƙasa da inganta rayuwar jama’a.

Source: Facebook
Hadimin Gwamna Radda kan harkokin yada labarai, Mustapha Samaila Ingawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamban 2026.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya nada sababbin kwamishinoni, mai magana da yawunsa ya samu babban mukami
Gwamna Radda ya je fada
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar girmamawa ga Sarkin Kudun Katsina kuma Hakimin Danja, Alhaji MT Bature, wanda Sarkin Fulani na Danja, Alhaji Yazid Danja, ya wakilta, a rana ta shida ta gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Dikko.
A jawabinsa na maraba, Shugaban Ƙaramar Hukumar Danja, Hon. Rabo Tambaya, ya yaba wa Gwamnan bisa jajircewarsa wajen inganta rayuwar al’ummar ƙaramar hukumar.
Nasarorin da gwamnatin Radda ta samu
Gwamna Radda ya bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannonin ilimi, kiwon lafiya, noma, tsaro da bunƙasa al’umma.
Ya bayyana ayyukan gine-gine da gyaran makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya, samar da kayan aikin noma, rarraba takin zamani a duk shekara, da kuma amincewa da alawus-alawus na wata-wata ga dagatai da shugabannin addini.
Gwamnan ya sanar da amincewar gwamnati na ɗaukaka matsayin Cibiyar Kiwon Lafiya zuwa Babban Asibitin Kiwon Lafiya, tare da cigaba da aikin samar da cibiyar samar da wutar lantarki ta hasken rana mai ƙarfin megawatt ɗaya a Dam ɗin Danja.
Haka kuma, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a ƙaddamar da aikin harkokin noman rani wanda ya haura dala miliyan 20, domin bunƙasa harkokin noma da samar da ƙarin damarmakin tattalin arziki ga manoma.
Gwamnan ya yaba da gudummawar Shirin Bunƙasa Al’umma (CDP) wajen ƙarfafa ci gaban ƙauyuka ta hanyar tallafin noma da samar da kayan aikin ban-ruwa, tare da jaddada cewa ingantaccen tsaro shi ne ginshiƙin dorewar ci gaba a yankin.
Radda ya nemi goyon baya ga Tinubu da APC
Ya kuma yi kira ga al’ummar Danja da su ci gaba da ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Jam’iyyar APC goyon baya a babban zaɓen shekarar 2027.
A nasa jawabin, Hakimin Danja ya nuna godiya ga Gwamna Radda bisa ayyukan raya ƙasa da sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, tallafin karatu da bunƙasa al’umma.
Ya kuma yaba wa Gwamnan bisa samar da damarmakin ci gaba ga al’ummar karamar hukumar Danja.

Source: Facebook
Abin da Radda zai yi kamfen da shi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa nasarorin da gwamnatinsa ta samu a faɗin jihar su ne ginshiƙin neman sabon wa’adi a zaɓen 2027.
Gwamna Radda ya bayyana hakan ne yayin babban taron yaƙin neman zaɓen Tinubu/Dikko na 2027 a Ƙaramar Hukumar Bakori.
Asali: Legit.ng
