An Fadi Sarakunan da Tinubu Ya Yarda a ba Su Manyan Motoci kafin 2027

An Fadi Sarakunan da Tinubu Ya Yarda a ba Su Manyan Motoci kafin 2027

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sayen sababbin motocin alfarma kirar SUV domin bai wa sarakunan gargajiya a Abuja
  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa za a bai wa sarakunan motocin kafin watan Disamba, yana mai cewa hakan na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa masarautu
  • Wike ya kuma sanar da cewa Tinubu ya amince da samar da motocin bas guda huɗu ga matasan Abuja domin ƙarfafa shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sayen sababbin motocin alfarma kirar SUV domin bai wa sarakunan gargajiya da aka ɗaukaka matsayinsu a babban birnin tarayya Abuja.

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin wani gangamin haɗin kan masu ruwa da tsaki na jam'iyyun siyasa da ƙaddamar da 'yan takarar majalisar tarayya a Abuja.

Kara karanta wannan

Yadda yar Chibok ta ki amincewa da iyayenta, ta nemi bin mijinta dan Boko Haram

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na jawabi. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa hadimar Wike, Rabi Musa Umar ta ce ministan ya ce matakin shugaban ƙasar ya nuna muhimmancin da yake bai wa sarakunan gargajiya wajen kiyaye al'adu da tabbatar da zaman lafiya.

Motocin da za a ba sarakuna

Wike ya bayyana cewa Tinubu ya amince da sayen motocin ne domin nuna girmamawa ga sarakunan gargajiya da kuma ƙarfafa matsayinsu a cikin al'umma.

Ya ce shugaban ƙasar ya kuma amince da ɗaukaka matsayin masarautun gargajiya a Abuja, bayan shafe shekaru 27 ba tare da an ɗauki irin wannan mataki ba.

Sanarwar ta ambato Wike yana cewa:

"Shugaban ƙasa ya ce ba za ku zama sarakuna da baki kawai ba. Ba za ku zama sarakuna kuna hawa babur mai kafa uku ko babur na haya ba. Da yardar Allah, kafin watan Disamba, kowannenku zai samu motar SUV."

Ya ƙara da cewa babu wata masarauta da ta fi buƙatar kulawa da ƙarfafawa kamar masarautun gargajiya na babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Dan Atiku ya faɗi dalilin fanɗarewa ubansa, ya ɗauki alƙawari ga Tinubu

Wike ya gargadi 'yan APC

Yayin da yake magana kan zaɓen 2027, Wike ya bukaci magoya bayan jam'iyyar APC da su tabbatar da cewa sun samu nasara a rumfunan zaɓensu, mazabunsu da ƙananan hukumominsu.

Ya ce bai kamata wani ya yi ikirarin cewa jam'iyyar ta yi nasara ba alhali ya sha kaye a rumfar zaɓensa, domin hakan na nuna bai bayar da gudummawa wajen nasarar jam'iyyar ba.

Ministan ya kuma yi gargaɗin cewa jam'iyyar ba za ta sake maimaita kuskuren da ta yi a zaɓen 2023 ba.

Nyesom Wike da Bola Tinubu
Nyesom Wike na gaisawa da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Wike ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Sanata Philip Tanimu Aduda zai lashe zaɓen Sanatan Abuja a watan Janairun 2027, yana mai cewa yana da kyakkyawar alaƙa da al'ummar yankin.

Baya ga motocin da aka ware wa sarakunan gargajiya, Wike ya bayyana cewa Tinubu ya kuma amince da samar da motocin bas guda huɗu ga matasan babban birnin tarayya.

Barau ya yabi Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Shugaba Bola Tinubu zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027.

Kara karanta wannan

An yi taru don hada kan 'yan adawa a kifar da Tinubu a gidan babban fasto

Barau ya bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da kwamitocin yaƙin neman zaɓe na ƙananan hukumomin Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado a jihar Kano.

Ya ce nazarin masana siyasa da yanayin siyasar Najeriya na yanzu sun nuna cewa Tinubu na da damar lashe zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng