Shugaban APC Ya Ji Dadin Giyar Mulki, Ya Cika Baki kan Girman Jam'iyyar a Najeriya

Shugaban APC Ya Ji Dadin Giyar Mulki, Ya Cika Baki kan Girman Jam'iyyar a Najeriya

  • Nentawe Yilwatda ya ce APC na da mambobi kusan miliyan 13 da tsare-tsaren shugabanci daga matakin ƙananan hukumomi har zuwa ƙasa
  • Ya bayyana cewa APC ce ke mulkin jihohi 31 cikin 36, tare da kujeru 88 a Majalisar Dattawa da 208 a Majalisar Wakilai
  • Yilwatda ya ce duk da ƙarfin APC, jam’iyyar ba za ta danne ’yan adawa ba, kuma za ta tabbatar da adalci a fafatawar dimokuraɗiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Netanwe Yilwatda, ya ce tsarin gudanarwa da ƙarfin ƙungiyoyin jam’iyyar sun sanya ta gaba sosai da sauran jam’iyyun siyasar Najeriya gabanin babban zaɓen 2027.

Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin tawagar binciken zaɓe ta ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), wadda tsohon mataimakin shugaban ƙasar Saliyo, Victor Foh, ya jagoranta.

Kara karanta wannan

2027: INEC ta mayar da sunan Pantami, an hango abin da hakan zai jawo ga mutanen Gombe

Farfesa Nentawe ya yi magana kan APC
Farfesa Nentawe Yilwatda na jawabi a wajen taro Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da Abimbola Tooki, mai taimaka wa shugaban APC kan harkokin yaɗa labarai, ya fitar ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamban 2026, ya ce taron ya gudana ne a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja, a ƙarshen mako, cewar rahoton TheCable.

APC na da mambobi miliyan 13

Yilwatda ya ce APC ta gina babbar rundunar siyasa mai tsari da haɗin kai, wadda ta bambanta ta da sauran jam’iyyu, tare da ba ta damar wayar da kan masu zaɓe da fafatawa yadda ya kamata a 2027.

Ya bayyana cewa APC ce jam’iyyar siyasa mafi girma a Najeriya, kuma babu wata jam’iyya da za ta iya kwatanta ƙarfinta ta fuskar tsari, shugabanci da yawan mambobi.

A cewarsa, APC ta ninka jam’iyyar da ke biye da ita girma kusan sau uku, inda take da mambobi kusan miliyan 13 da suka yi rajista a faɗin ƙananan hukumomin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya gano hanyar da Tinubu zai samu kuri'u cikin sauki a 2027

Ya ƙara da cewa jam’iyyar tana da zaɓaɓɓu da waɗanda aka naɗa a muƙaman shugabanci tun daga matakin rumfunan jam’iyya, ƙananan hukumomi da jihohi har zuwa matakin ƙasa.

Yawan kujerun APC a majalisun dokoki

Shugaban APC ya kuma bayyana cewa jam’iyyar tana mulkin jihohi 31 daga cikin 36 na Najeriya, yayin da take da kujeru 88 cikin 109 a Majalisar Dattawa.

Haka kuma, ya ce APC tana da wakilai 208 cikin kujeru 360 na Majalisar Wakilai, lamarin da ya bayyana a matsayin hujjar irin ƙarfin da jam’iyyar ke da shi a fagen siyasar ƙasar.

Yilwatda ya ce waɗannan tsare-tsare su ne ginshiƙin ƙarfin APC, domin suna ba ta damar isa ga al’ummar Najeriya a sassa daban-daban da kuma fahimtar buƙatunsu.

APC ta yi alƙawarin ba wa ’yan adawa dama

Duk da bayyana ƙarfin jam’iyyarsa, Yilwatda ya shaida wa tawagar ECOWAS cewa APC na nan daram wajen bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya da kuma tabbatar da sahihiyar fafatawar siyasa.

Ya ce jam’iyyar ba za ta yi amfani da matsayinta wajen murƙushe ’yan adawa ba, domin dukkan jam’iyyun siyasa na da haƙƙin samun dama iri ɗaya wajen gabatar da manufofinsu ga masu zaɓe.

Kara karanta wannan

Gwamnan da ke goyon bayan Tinubu a 2027, ya watsa wa APC kasa a ido

Ya jaddada cewa ya kamata a bai wa dukkan jam’iyyu damar amfani da kafafen yaɗa labarai, wuraren gudanar da gangamin siyasa da sauran hanyoyin da doka ta amince da su.

A ƙarshe, Yilwatda ya kawo zanga-zangar da aka gudanar kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin misali na yadda ’yan Najeriya da ƙungiyoyin adawa ke da damar bayyana ra’ayoyinsu.

Nentawe ya yi magana kan APC
Farfesa Nentawe Yilwatda na jawabi a wajen taron APC Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Facebook

Nentawe ya hango nasarar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Nentawe ya bayyana cewa ayyukan more rayuwa da gwamnatin Shugaba Tinubu ke gudanarwa za su taimaka wa jam’iyyar wajen samun ƙuri’u a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng