"Ka cika alkawari"; Basarake ya yi wa Gwamna Radda albishir
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, da tawagarsa sun ziyarci karamar hukumar Faskari a ci gaba da rangadin da yake yi
- A yayin ziyarar, Sarkin Yamman Katsina kuma Hakimin Faskari, ya kwararo yabi ga gwamnan kan alkawuran da ya cika wa mutanen yankin
- Ya bayyana cewa Gwamna Radda ya cika masu alkawuran da ya dauko bakin gwargwado a kakar zaben shekarar 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Sarkin Yamman Katsina kuma Hakimin Faskari, Engr. Alhaji Aminu Tukur Usman Sa’ad, ya yabawa Gwamna Malam Dikko Umaru Radda.
Hakimin na Faskari ya yaba wa Gwamna Radda ne bisa cika alkawuran da gwamnatinsa ta dauka ga al’ummar Karamar Hukumar Faskari lokacin yakin neman zaben kakar da ta gabata.

Source: Facebook
Hadimin Gwamna Radda kan harkokin kafafen yada labarai, Mustapha Samaila Ingawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook ranar Asabar, 31 ga watan Oktoban 2026.
Gwamna Radda ya samu yabo
A cewar sanarwar, Hakimin ya bayyana hakan ne lokacin da Gwamna Radda ya kai masa ziyarar girmamawa a rana ta hudu ta yakin neman zaben Tinubu/Dikko na 2027.
“A lokacin yakin neman zaben 2023, mun bukaci tsaro, babban asibiti, aikin samar da ruwa da kuma dam da sauran abubuwan more rayuwa. A yau, muna farin ciki da cewa kun samar da wadannan ayyuka gwargwadon iyawarku.” In ji shi.
Ya gode wa Gwamnan bisa gina babban asibiti, dam, hanyar Sheme–Faskari da sauran muhimman ayyukan more rayuwa.
Haka kuma, ya yaba da sauye-sauyen da aka kawo a hukumomin gargajiya, shirye-shiryen bayar da tallafin karatu, Shirin Cigaban Al’umma (CDP), tallafin noma da inganta cibiyoyin kiwon lafiya da ilimi.
Gwamna Radda ya fadi ayyukan da ya yi
A nasa jawabin, Gwamna Radda ya bayyana nasarorin gwamnatinsa a fannonin kiwon lafiya, samar da ruwa, tsaro, bunkasa noma da karfafa tattalin arzikin al’umma, ciki har da gina gidaje ga ‘yan gudun hijira daga muhallansu tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya.
Gwamna Radda ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na karfafa hukumomin gargajiya da na addini, tallafa wa manoma ta hanyar raba takin zamani a duk lokacin damina, da kuma fadada shirye-shiryen cigaban al’umma.
Ya bukaci ci gaba da goyon bayan hukumomin gargajiya da al’ummar Faskari ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC a babban zaben 2027.

Source: Facebook
An farmaki 'yan APC a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin hankali a garin Malumfashi na Jihar Katsina bayan hari kan wasu magoya bayan jam’iyyar APC.
Yan jam'iyyar sun ce wasu matasa sun kai musu hari yayin da suke tafiya Funtua domin halartar taron yaƙin neman zaɓen Tinubu–Dikko yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaben shekarar 2027.
Waɗanda abin ya shafa sun shaida cewa suna cikin ayarin motocin Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, lokacin da wasu gungun matasa suka tare su tare da kai musu hari.
Asali: Legit.ng

