Shawara Mai Kama Hankali da Sheikh Gumi Ya ba Ƴan Siyasa a Najeriya
- Sheikh Ahmad Gumi ya bukaci jam'iyyun siyasa su gargadi magoya bayansu kan guje wa tashin hankali, barazana da lalata dukiyoyi yayin yakin neman zaben 2027
- Malamin ya ce tashin hankali ba ya samar da kuri'u, yana mai cewa hakan na korar masu kada kuri'a daga rumfunan zabe
- Gumi ya yi gargadin ne yayin da ake samun karuwar hare-hare da rikice-rikicen siyasa a wasu jihohin Najeriya gabanin babban zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci dukkan jam'iyyun siyasa ana daf da gudanar da zabe.
Sheikh Gumi ya bukaci 'yan takara su gargadi magoya bayansu kan guje wa tashin hankali, barazana da lalata dukiyoyi yayin yakin neman zaben 2027.

Source: Twitter
Gumi ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba, 2026.
Malamin ya yi nuni da karancin masu kada kuri'a a zaben shugaban kasa na 2023, inda ya ce tashin hankali ba ya taimakawa wajen samun nasarar zabe.
Gumi ya bayyana illar tashin hankali a zabe
A cewar malamin, daga cikin masu rajistar zabe 93,469,008 a shekarar 2023, mutum 24,965,218 ne kawai suka kada kuri'a, wanda ya kai kashi 26.71 cikin 100.
Ya kara da cewa kashi 73.29 cikin 100 na masu rajistar ba su kada kuri'a ba, yana mai cewa hakan na nuna yadda tsoratar da jama'a ke hana su shiga harkokin zabe.
Gumi ya ce:
"Ina zaben shugaban kasa na Najeriya na shekarar 2023, daga cikin masu rajistar zabe 93,469,008, mutum 24,965,218 ne kawai suka kada kuri'a, wato kashi 26.71 cikin 100. Wannan na nufin kashi 73.29 cikin 100 ba su kada kuri'a ba.
"Wannan lamari na yawan faruwa, inda mafi yawan jama'a ke kaurace wa zabe. Don haka, dukkan jam'iyyun siyasa da 'yan takara dole ne su gargadi magoya bayansu masu tsananin kishin jam'iyya kan lalata dukiyoyi, tsoratarwa da tashin hankali yayin wannan yakin neman zabe.
"Tashin hankali ba ya samar da kuri'u, illa kawai yana korar masu kada kuri'a tare da raunana dimokuradiyya."

Source: Twitter
Ana samun karuwar rikicin siyasa a Najeriya
Gargadin Sheikh Gumi na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karuwar rikice-rikicen siyasa gabanin babban zaben shekarar 2027.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dage dokar hana yakin neman zabe a ranar 19 ga watan Agustan 2026, amma a wasu jihohi ana samun rikici maimakon fafatawa ta hanyar manufofi da akidu.
Rahoton kwamitin zaman lafiya na kasa da ya shafi lokacin daga 19 ga Agusta zuwa 27 ga Oktoba ya bayyana cewa rikicin siyasa da amfani da 'yan daba ne suka fi yawa, inda aka samu rahotanni 33.
Gumi ya magantu kan harin ƴan bindiga
Mun ba ku labarin cewa Sheikh Ahmad Gumi ya ce wasu ’yan bindiga sun bayyana masa cewa ba sa farin cikin kashe-kashen, amma suna ganin an tilasta musu ci gaba da kai hare-hare.
Malamin ya ce ’yan bindigar na kallon rikicin a matsayin ramuwar gayya tsakanin su da al’ummomin da ke kai musu hare-hare.
Gumi ya bayyana cewa tsoron kada a kashe su idan sun ajiye makamai na daga cikin dalilan da ke hana su mika wuya.
Asali: Legit.ng

