A Karon Farko Mataimakin Gwamnan Sokoto Ya Magantu Kan Sauya Sheka Zuwa APC

A Karon Farko Mataimakin Gwamnan Sokoto Ya Magantu Kan Sauya Sheka Zuwa APC

  • Alhaji Manir Muhammad Dan'iya, mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya yi magana game da rade-radin yana shirin komawa jam'iyyar APC
  • Hakan ya biyo bayan rasa samun tikitin takarar gwamna da ya yi ne inda Tambuwal da jiga-jigan PDP a Sokoto suka zabi tsohon sakatern gwamnatin jihar, Sa'idu Umar Ubandoma
  • Manir ya ce mutane su zuba ido su ga abin da zai faru sai dai ya kuma yi kira garesu da su zabi jam'iyyar PDP a babban zaben shekarar 2023 da ke tafe

Jihar Sokoto - Mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Manir Muhammad Dan'iya, a karon farko ya yi magana kan jita-jitan da ke yawo cewa yana daf da sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC), rahoton Daily Trust.

JIhar Sokoto
A Karon Farko Mataimakin Gwamnan Sokoto Ya Magantu Kan Sauya Sheka Zuwa APC. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

Komawa APC: Ku zuba ido ku gani - Munir Dan'iya

Kara karanta wannan

Mashawarcin Gwamnan Arewa Na Musamman, Shahararren Jigon PDP, Sun Koma APC Gabanin Babban Zaben 2023

Daily Trust ta rahoto cewa yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai a taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a ranar Alhamis, ya yi tambaya, ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yaushe ne abin zai faru?"

Ya kara da cewa:

"Ka ce jita-jita ne, don haka ka jira ka gani."

An ce, Dan'iya, wanda shine dan takarar kujerar sanata na mazabar Sokoto North, ya yi fushi bisa matakin da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da sauran masu ruwa da tsaki a PDP suka dauka na zaben tsohon sakataren gwamnatin jihar, Sai'du Umar Ubandoma, a matsayin dan takarar gwamna na jam'iyyar.

Hakan ya ci karo da al'adar siyasa inda galibi mataimakin gwamna ake zabe ya gaji kujerar gwamna.

Munir ya bukaci mutanen Sokoto su zabi APC a zaben 2023

Amma, ya yi kira ga mutanen jihar su zabi jam'iyyar PDP a babban zaben da ke tafe.

Kara karanta wannan

PDP Ta Sha Alwashin Yi Wa Gwamnan Babban Jihar Arewa Ritaya Zuwa Saudiyya A 2023

Ya ce:

"Mun gayyaci masu ruwa da tsaki don tattaunawa da su don sanin matsalolinsu, kuma mun fara magance wasu daga cikinsu."

Bafarawa ya nuna cewa yana fatan PDP za ta yi nasara a zaben.

Jiga-jigan jam'iyyar PDP a Jihar Sokoto Sun Koma APC

Wasu manya cikin masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP a Sokoto sun fita daga jam'iyyar sun koma jam'iyyar hamayya ta APC.

Jam'iyyun siyasan na APC da PDP na cigaba da fuskantar kaura a cikin yan kwanakin nan yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel