Tallafin Mai: ADC Ta Sake Albishir ga Ƴan Najeriya kan Shirin Atiku bayan Hawa Mulki
- ADC ta bayyana cewa Atiku Abubakar zai sayar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida a farashi mai rahusa domin rage kuɗin samar da fetur
- Uche Diala ya ce shirin tallafin samarwa zai bambanta da tallafin man fetur da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje ko bayar da ɗanyen mai kyauta
- ADC ta ce Atiku zai amince da sakamakon zaɓen 2027 idan aka kayar da shi cikin adalci, amma tana da kwarin gwiwar zai yi nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi magana kan shirin Atiku Abubakar ga yan Najeriya.
ADC ta bayyana cewa ɗan takararta, Atiku Abubakar, zai ware wani kaso na ɗanyen man Najeriya domin sayarwa ga matatun cikin gida a farashi mai rahusa, a matsayin wani ɓangare na shirin tallafin samarwa.

Source: Twitter
Ɗaya daga cikin kakakin majalisar, Dakta Uche Diala ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels.
Diala ya ce wannan shiri zai rage kuɗin sayen ɗanyen mai da matatun za su riƙa kashewa.
Ya bayyana cewa shirin ya bambanta da tallafa wa man fetur da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje ko kuma bayar da ɗanyen mai kyauta ga masu matatun.
Ya ce:
“Muna cewa, gwargwadon bukatar ‘yan Najeriya na amfani da kayayyaki da gudanar da rayuwarsu, za mu sayar da kaso namu na ɗanyen mai ga matatun cikin gida da suka shiga shirin a farashi mai rahusa.
“Ba za su saye shi a farashin duniya ba, amma kuma ba za su same shi kyauta ba. Wannan tallafin samarwa ne a ɓangaren samar da mai, ba tallafin amfani da shi ko shigo da shi daga ƙasashen waje ba.”
Da aka tambaye shi yadda za a ci gaba da gudanar da shirin, Diala ya ce gwamnati za ta fara tantance yawan ɗanyen man da ake da shi domin amfanin cikin gida bayan cire kaso na yarjejeniyoyin haɗin gwiwa da sauran wajibai.
Ya ce:
“Muna buƙatar sanin yawan ɗanyen man da muke da shi, sannan daga nan za mu fara da yarjejeniyoyin haɗin gwiwa.”
Ya ƙara da cewa dokar masana’antar man fetur ta ƙasa, wato Petroleum Industry Act, ta tanadi samar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida.
Diala ya bayyana cewa shirin zai kuma buƙaci sake duba yarjejeniyoyin da ake da su, ciki har da yarjejeniyoyin sayar da mai tun kafin lokacin samar da shi, tare da ƙara yawan man da ake haƙowa.
Ya yi nuni da cewa kasafin kuɗin shekarar 2026 ya yi hasashen samar da ganga miliyan 1.8 na ɗanyen mai a kowace rana, yana mai cewa Najeriya za ta iya ƙara yawan man da take samarwa domin dorewar shirin.
Diala ya kuma ƙaryata zargin cewa ma’aikatan ADC sun shafe watanni ba tare da karɓar albashi ba, inda ya bayyana zargin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi a matsayin ƙirƙirarren labari.
ADC ta fadi tsarin kamfen Atiku
Mun ba ku labarin cewa daraktan yada labaran kamfen ADC, Phrank Shaibu ya bayyana shirin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kan yakin neman zabensa.
Shaibu ya bayyana cewa yakin neman zaben ba zai tsaya ga manyan biranen jihohi da gangamin siyasa kawai ba.
Ya ce matsin tattalin arziki da yunwa matsaloli ne da suka shafi ’yan Najeriya a ko’ina, ba tare da la’akari da yankin da suke zaune ba.
Asali: Legit.ng


