'Yan Sanda Sun Lallaba Otel Sun Kama Tsohon Gwamna a Najeriya

'Yan Sanda Sun Lallaba Otel Sun Kama Tsohon Gwamna a Najeriya

  • ’Yan sandan Najeriya sun kama tsohon gwamnan Imo, Sanata Rochas Okorocha, a wani otal da ke Abuja bisa zargin hada baki wajen aikata laifi
  • Rahotanni sun ce kamen ya biyo bayan zargin cewa Okorocha ya kasa amsa gayyatar ’yan sanda sau da dama yayin da ake gudanar da bincike
  • Okorocha ya musanta cewa wata kotu ta bayar da umarnin kama shi, yana mai kalubalantar wadanda suka yada labarin da su fitar da takardar umarnin kotun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Rahotanni sun bayyana cewa jami’an rundunar ’yan sandan Najeriya sun kama tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, a daren Litinin, 12 ga Oktoba, 2026, a otal din REIZ da ke Abuja.

Ana zargin tsohon gwamnan da hada baki wajen aikata laifi, kitsa takardun karya da kuma yin kwaikwayon wani mutum.

Kara karanta wannan

Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami

Rochas Okorocha a wani waje
Tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha. Hoto: Rochas Okorocha
Source: Facebook

The Sun ta wallafa cewa kamen ya biyo bayan zargin cewa Okorocha ya yi watsi da gayyatar ’yan sanda sau da dama dangane da wani bincike da ake gudanarwa, lamarin da ya sa aka nemi umarnin kotu na kama shi.

Yadda aka gayyaci Okorocha

Rahotannin sun nuna cewa ’yan sanda sun fara gayyatar Okorocha zuwa hedikwatar rundunar da ke Abuja ranar 2 ga Satumba, 2026.

Sai dai an dage ganawar zuwa ranar 8 ga Satumba bisa bukatar lauyoyinsa, amma rahoton ya ce bai halarci ganawar a ranar da aka sanya ba.

Wannan batu ya zo ne a daidai lokacin da Okorocha ya musanta rahotannin da ke cewa wata kotu ta bayar da umarnin kama shi.

Maganar da Okorocha ya yi

A wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa kuma mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Sam Onwuemeodo, ya sanya wa hannu, Okorocha ya ce babu wata kotu, ko ta majistare ko Babbar Kotu, da ta bayar da umarnin kama shi.

Kara karanta wannan

Tsohuwar gaba ta yi kamari: Wike ya yi wa Amaechi mummunan baki a siyasa

This Day ta wallafa cewa sanarwar ta mayar da martani ga wani rahoto da ya yi ikirarin cewa wata kotun majistare da ke Abuja ta bayar da umarnin kama Okorocha da Ifeanyi Ararume.

Rahoton ya alakanta umarnin da korafin da Kwamishinan Zabe na INEC a Imo, Chukwuemeka Ibejiako, ya aikawa ’yan sanda da (DSS), inda ya bukaci a binciki Okorocha da wasu kan zargin gabatar da sakamakon zaben fitar da gwani na APC na bogi.

Sai dai tawagar Okorocha ta ce rahoton ya kunshi babban sabani a ranakun da aka ambata.

Sanarwar ta ce:

“An rubuta korafin ne ranar 8 ga Oktoba, 2026, kuma lambar shari’ar da aka ambata ita ce CR/M/084/2026, amma aka ce an bayar da umarnin kama shi tun wata guda kafin hakan.
“A takaice, an bayar da umarnin kotu kafin a gabatar da korafin, kuma kafin a shigar da karar.”
Taswirar FCT, Abuja
Taswirar FCT, Abuja a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

An kama dan siyasa a Yobe

A wani labarin, kun ji cewa sojojin Najeriya sun kama wani dan siyasa a jihar Yobe mai suna Wakiil Mama, wanda aka fi sani da Mai Salati

Kara karanta wannan

Kotu ta nemi cafke tsohon gwamna da sanata, an gano rashin gaskiyarsu kan zabe

An kama Mai Salati ne bayan sojoji sun gano wani yunkuri na ba jami’an tsaro cin hanci domin sakin wasu da aka kama da zargin samar da kayan tallafi ga ’yan ta’adda.

A cewar rahoton, kama dan siyasar ya biyo bayan wani aikin leken asiri da sojoji suka jagoranta domin gano dan siyasar da kama shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng