'Gyaran da Peter Obi Zai Yi a Bangaren da Tinubu Ya Nakasa a Najeriya’
- Pat Utomi ya bayyana cewa Peter Obi na shirin farfado da darajar Naira zuwa N500 kan kowace dala idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027
- Utomi ya ce shirin zai taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki, talauci da tsadar rayuwa, tare da kara karfin sayen kayan masarufi ga 'yan Najeriya
- Ya yi hasashen cewa farashin burodin N1,750 zai koma N800, shinkafa N55,000 ta koma N27,500, yayin da sauran kayan abinci za su sauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jigo arzikin a jam'iyyar NDC, Pat Utomi, ya yi magana kan shirin Peter Obi idan ya hau mulkin Najeriya.
Ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Peter Obi, na shirin karfafa darajar Naira zuwa N500 kan kowace dala idan aka zabe shi a 2027.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis 29 ga watan Oktobar 2026.
Yadda Obi ke son dawa da darajar Naira
Ya ce shirin karfafa Naira daga kimanin N1,350 zuwa N500 kan dala zai taimaka wajen shawo kan hauhawar farashin kayayyaki, rage talauci da kara karfin sayen kayan masarufi ga 'yan Najeriya.
Ya rubuta cewa:
“Mun yi imanin cewa mayar da karfafa darajar musayar kudi zuwa wani muhimmin buri, ta hanyar karfafa Naira daga N1,350 zuwa N500 kan dala a matsayin wani bangare na tsarin manufofinmu, dabara ce da za ta taimaka mana samun nasara.
“Wannan shiri zai samar da hanyoyi daban-daban na rage hauhawar farashin kayayyaki, rage talauci da kuma saukaka tsadar rayuwa kai tsaye.”

Source: Facebook
Hasashen da aka yi kan kayan masarufi
Utomi ya yi hasashen cewa burodin da ake sayarwa a kan N1,750 a yanzu zai iya komawa N800, yayin da buhun shinkafar waje mai nauyin kilo 50 zai sauka daga N55,000 zuwa N27,500.

Kara karanta wannan
Sauki zai zo: Yadda Peter Obi zai saukar da farashin kayayyaki idan ya zama shugaban kasa
Haka kuma, ya ce farashin doya mai matsakaicin girma zai sauka daga N2,400 zuwa N1,200, yayin da buhun masara mai nauyin kilo 50 zai koma N37,500 daga N75,000.
Utomi ya kara hasashen cewa damin ayaba zai sauka daga N2,500 zuwa N1,250, yayin da farashin cikakkiyar kaza zai ragu daga N7,000 zuwa N3,500.
Ya ce kwai guda 12 za su koma N1,150 daga N2,300, yayin da fentin garin rogo (garri) zai sauka daga N1,300 zuwa N650.
Utomi ya bayyana cewa wannan kudiri ya nuna jajircewar jam'iyyar wajen inganta rayuwar al'umma, musamman 'yan Najeriya da ke fama da matsanancin talauci ta fannoni daban-daban.
Ya kara da cewa:
“Wannan ya nuna karara shirinmu na zahiri na inganta rayuwar 'yan Najeriya miliyan 140 da ke fama da talauci ta fannoni daban-daban.”
Obi zai yi aiki da Kwankwaso
Mun ba ku labarin cewa dan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso idan suka lashe zaɓen 2027.
Obi ya ce gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga tsaro da ilimi, tare da ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren ilimi domin magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.
Kwankwaso ya buƙaci ’yan Najeriya su haɗa kai, su fita kaɗa ƙuri’a tare da kare ƙuri’unsu, yayin da Sanata Victor Umeh ya bayyana tikitin Obi-Kwankwaso a matsayin mafi dacewa.
Asali: Legit.ng
