Masu Shirin Magudin Zabe Sun Shiga Uku, Obi Ya Yi Barazana ga INEC
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi barazanar hukunta duk wanda ya yi magudin zaɓe
- Obi ya ce jami’an INEC da duk masu hannu a gudanar da zaɓe da aka samu da laifin maguɗi za su fuskanci ɗaurin kurkuku
- Tsohon gwamnan Anambra ya kuma buƙaci tsaurara dokokin cancantar tsayawa takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya nuna damuwa game da shirin magudin zabe.
Obi ya yi barazanar ɗaukar mataki kan duk wanda ya yi magudin zaɓe a Najeriya, yana mai cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da hukunta masu laifin idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Source: Facebook
Magudin zabe: Peter Obi ya yi barazana
Obi ya bayyana hakan ne ranar Laraba a wani taron tattaunawa da magoya bayan jam’iyyar NDC a Jihar Nasarawa, cewar Punch.

Kara karanta wannan
"Bai cancanta ba," An tono abin da zai iya zama matsala ga abokin takarar Atiku a 2027
Da aka tambaye shi matakin da jam’iyyar za ta ɗauka kan magudin zaɓe, tsohon gwamnan Anambra ya ce ba za su bari a yi magudin zaɓe ba tare da ɗaukar mataki ba a zaɓe mai zuwa.
Ya ce:
“Ba ku tambaye ni abin da za mu yi idan mutane suka yi magudin zaɓe a shekara mai zuwa ba. Bari na tabbatar muku, abu na farko, a zaɓe mai zuwa, za mu yi magudin waɗanda suka yi magudin zaɓe.”
Obi ya ƙara da cewa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa, zai tabbatar da cewa ba wanda zai iya yin magudin zaɓe a ƙarƙashin gwamnatinsa, ta hanyar ƙarfafa jam’iyyun siyasa da sake fasalin tsarin zaɓe.
Ya ce:
“Kuma bari na tabbatar muku da abu na biyu, idan aka zaɓe ni shugaban ƙasar Najeriya, babu wanda zai sake yin magudin zaɓe a wannan ƙasa, domin abu na farko da ya kamata mu yi shi ne ƙarfafa jam’iyyunmu da kuma tsarin zaɓe.”
Obi ya nemi tsaurara dokokin tsayawa takara
Ɗan takarar ya kuma yi kira da a tsaurara dokokin da ke tsara cancantar tsayawa takara, yana mai cewa ya kamata a buƙaci duk mai son yin takara ya nuna cewa ya halarci makarantar firamare da sakandare.
Obi ya ce:
“Dokokinmu za su kasance masu tsauri. Domin ka tsaya takara, dole ne ka halarci makarantar firamare da sakandare, kuma hakan ya zama a bayyane kuma a tabbatar da shi.”
Ya yi gargaɗin cewa duk wanda bai halarci waɗannan makarantu ba, ko kuma ya ƙirƙiri takardar shaidar karatu, zai fuskanci ɗaurin kurkuku.

Source: Facebook
Jami’an INEC za su su fuskanci hukunci
Obi ya faɗaɗa gargaɗinsa ga jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da sauran waɗanda ke da hannu a gudanar da zaɓe, yana mai cewa duk wanda aka samu da laifin magudin zaɓe a ƙarƙashin gwamnatinsa zai fuskanci hukunci.
Obi ya bayyana cewa tsarin da yake son kafawa zai dogara ne kan bin doka da oda, yana mai cewa babu wanda ya kamata a keɓe daga ɗaukar alhakin ayyukansa, ko da kuwa matsayinsa a ƙasa.
Ya ce:
“Duk wani jami’in INEC ko wani mutum da ke da hannu a zaɓe a ƙarƙashin gwamnatina wanda ya yi magudin zaɓe, zai tafi kurkuku.
“A ƙarƙashin gwamnatina, dole ne Najeriya ta zama ƙasa mai bin doka, kuma kowa, tun daga mutum na farko har zuwa na ƙarshe, dole ne ya bi doka.
"Babu wanda ya fi ƙarfin doka, kuma babu wanda zai riƙa aikata abin da ya ga dama.”
Abin da Obi ya dura kan Gwamnatin Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Peter Obi ya ce Shugaba Bola Tinubu ya kamata ya bar mulki a 2027, yana zargin gwamnatinsa da ƙara taɓarɓarewar matsalolin tattalin arzikin Najeriya.
Obi ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Abuja, yayin ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar NDC ta ƙasa.
Tsohon gwamnan Anambra ya ce Najeriya na fuskantar matsala a ƙarƙashin shugabancin Tinubu, yana mai cewa ’yan Najeriya na neman sabon shugabanci.
Asali: Legit.ng

