Arewa Ta Tinubu Ce: Gwamna Zai Tallata Shugaban Ƙasa Gida Gida a Zaɓen 2027

Arewa Ta Tinubu Ce: Gwamna Zai Tallata Shugaban Ƙasa Gida Gida a Zaɓen 2027

  • Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya ƙaddamar da ƙungiyar PBAT Door-to-Door domin tallafa wa sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Tompolo ya bayar da motocin kamfen guda 25 domin ƙarfafa yaɗa manufofin Tinubu da tattara magoya baya a ƙananan hukumomin Plateau
  • Mutfwang ya sanar da cewa Tinubu zai kai ziyara Plateau ranar 14 ga Nuwamba 2026, inda za a gudanar da babban gangami a Jos

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya ƙaddamar da reshen jihar na ƙungiyar PBAT Door-to-Door Movement a jihar.

Gwamna Caleb ya kaddamar da kungiyar ce domin goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Gwamna ya kaddamar da kamfen din Tinubu
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga, Caleb Mutfwang.
Source: Twitter

An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a Langfield Event Centre da ke Little Rayfield, Jos, cewar Punch.

An kaddamar da motocin kamfen Tinubu

Kara karanta wannan

Obi ya bukaci Bola Tinubu ya koma gida ya huta, ya bar maganar takarar 2027

An kuma ƙaddamar da motocin kamfen guda 25 da babban majiɓincin ƙungiyar, Cif Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, ya bayar.

Da yake jawabi a wajen taron, Mutfwang ya ce shawarar da ya yanke na goyon bayan Tinubu ta samo asali ne daga ganawar da ya yi da shugaban ƙasar bayan zaɓen 2023.

Ya ce:

“Na yanke shawarar cewa wannan shi ne shugaban ƙasar da zan yi aiki tare da shi, duk da cewa ba mu jam’iyya ɗaya ba a lokacin. Na ga mutum mai ƙudurin kyautata Najeriya.”

Gwamnan ya amince cewa ƙasar na fuskantar ƙalubalen tattalin arziki da tsaro, amma ya ce gwamnatin tarayya ta ɗauki matakai domin magance su, yana kira ga ’yan Najeriya su yi haƙuri yayin da sauye-sauyen ke tasiri.

Ya bayyana cewa:

“Eh, har yanzu ba mu kai inda muke so ba. Akwai ƙalubale a ƙasar, kuma ba za mu musanta hakan ba. Amma tabbas, muna kan hanyar gyara abubuwa.”
Gwamna Caleb ya magantu kan rashin tsaro
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau. Hoto: Caleb Mutfwang.
Source: Twitter

Gwamna Caleb ya magantu kan tsaro

Dangane da tsaro, Mutfwang ya yaba wa Tinubu bisa goyon bayan da yake bai wa Plateau, yana mai cewa haɗin gwiwar gwamnatocin tarayya da jiha zai taimaka wajen wargaza ƙungiyoyin masu aikata laifuka da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya sake neman alfarmar yan Najeriya yayin kamfen a Kaduna

Ya kuma ambaci aikin da gwamnatin tarayya ke shirin yi na faɗaɗa hanyar Mararaban Jama’a–Mangu–Pankshin–Langtang–Shendam, wadda za ta zarce ta tsallaka Kogin Ibi, a matsayin alamar ƙudurin gwamnati na magance matsalolin ci gaba da suka daɗe suna addabar jihar.

A cewarsa, tawagar ƙwararru daga Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta riga ta isa jihar domin gudanar da ayyukan farko na shirin hanyar. Ya bayyana fatan kammala shirye-shiryen da suka dace kafin ƙarshen shekarar nan.

Gwamnan ya ce aikin zai zama babban sauyi ga al’ummomin da suka shafe shekaru masu yawa suna fama da munanan hanyoyi. Ya ƙara da cewa faɗaɗa hanyar da samar da matakan kariya za su inganta zirga-zirga tare da bunƙasa tattalin arziki.

Uba Sani ya shirya tallata Tinubu

Mun ba ku labarin cewa Uba Sani ya ce ba zai yi nadamar goyon bayan Tinubu ba, kuma zai ci gaba da mara masa baya har zuwa ƙarshen lokacin yaƙin neman zaɓe.

Gwamnan ya danganta goyon bayansa ga alaƙar siyasa da ke tsakaninsu tun shekarar 1994, lokacin gwagwarmayar dawo da mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya.

Ya ce amincewa da wasu manyan ayyukan jami'o'i da gyaran hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari na daga cikin abubuwan da suka amfani jihar a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.