Rashin Tsaro Ya Yi Kamari, Limaman Masallatan Juma’a Sun Yi Magana da Murya 1

Rashin Tsaro Ya Yi Kamari, Limaman Masallatan Juma’a Sun Yi Magana da Murya 1

  • Malaman addinin Musulunci biyar a Plateau, sun koka kan barazanar tsaro, tare da roƙon gwamnatin tarayya ta gaggauta shiga tsakani
  • Limaman sun zargi jami’an tsaro da kama wasu mambobinsu ba tare da hujja ba, lalata dukiyoyi da kona gidaje a yankunansu
  • Sun bukaci gwamnati ta tabbatar da adalci, kare al’ummominsu da wuraren ibada, tare da dakatar da kashe-kashe da hare-hare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Barikin Ladi, Plateau - Limaman masallatan Juma’a biyar daga Dorowa-Babuje, Luggere da Jol da ke ƙaramar hukumar Barikin Ladi a Plateau, sun nuna damuwa kan barazanar tsaro.

Limaman sun hada da Bashir Khamis, Salihu Muhammad, Idris Usman, Aliyu Mahmud da Yahaya, wadanda suka ce matsalolin tsaro na ƙara tayar musu da hankali.

Limamai sun koka kan matsalar tsaro
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau. Hoto: Caleb Mutfwang.
Source: Twitter

Limamai sun nemi taimakao kan tsaro

Da yake magana yayin ziyarar da suka kai ofishin jaridar Daily Trust da ke Jos ranar Talata, Imam Yahaya na Masallacin Juma’a da ke Luggere, ya bayyana cewa halin da ake ciki na da matukar tayar da hankali

Kara karanta wannan

Mutane sun bar kasuwancinsu da noma baki daya domin alhinin tsohon gwamna

Wannan na zuwa ne yayin da ake fama da tashin hankali a ƙananan hukumomin Barkin Ladi, Mangu, Bokkos da Riyom, inda gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita daga yamma zuwa wayewar gari domin dawo da zaman lafiya bayan kashe-kashe da hare-hare.

Saboda damuwarsu kan halin da ake ciki, limaman sun bukaci gwamnati ta dauki matakan magance matsalolin kafin su ta'azzara.

Sun ce akwai bukatar jawo hankalin gwamnatocin jiha da tarayya kan barazanar da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya a yankin.

Ya ce:

“Muna cikin mawuyacin hali a wadannan al’ummomi. Kama mambobinmu ba bisa ka’ida ba, ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, ya zama ruwan dare. Ana kama tawagar kafofin sada zumunta da ke taimaka mana wajen sanar da duniya halin da muke ciki, sannan ana yi wa wasu barazana.
“Jami’an tsaro na lalata dukiyoyi, yayin da ake yawan kashe mutane da dabbobi a kullum. Ana kai hare-hare kan al’ummomi tare da kona gidaje ba tare da wani dalili ba.”

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da sojojin Najeriya suka tare wasu matasa, suka harbe su har lahira

A cewar limaman, ba sa adawa da duk wani bincike da ya dace da doka ko kuma jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu, amma sun bukaci a yi adalci da nuna rashin son kai wajen mu’amala da su da makwabtansu.

Yahaya ya ce:

“Muna rokon a rika yi mana adalci kamar yadda ake yi wa makwabtanmu Kiristoci, kuma kada a bar duk wanda aka samu da laifi ya kauce wa hukunci, ba tare da la’akari da kabila ko addininsa ba.
“Muna kuma rokon jami’an tsaro su daina lalata mana dukiyoyi da kona gidajenmu. Muna bukatar tsaro a cikin al’ummominmu da wuraren ibadarmu yayin gudanar da sallar Juma’a. Haka kuma, jami’an tsaro su bar dabbobi su samu damar kiwo.”

Yan bindiga sun kai hari a Plateau

An ji cewa wasu ’yan bindiga sun kashe wani jami’in hukumar tsaro ta NSCDC tare da yin garkuwa da wani ɗan kasuwa a Plateau.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare ranar Litinin, bayan maharan sun sace ɗan kasuwar da ke sana’ar mai, siminti da takin zamani.

Al’ummar yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da gwamnatin jihar Filato da su ƙara tsaurara matakan tsaro tare da tabbatar da kuɓutar ɗan kasuwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.