'Abubuwan da Yan Najeriya Za Su Duba kafin Su Yanke Hukuncin Sake Zaben Tinubu a 2027'

'Abubuwan da Yan Najeriya Za Su Duba kafin Su Yanke Hukuncin Sake Zaben Tinubu a 2027'

  • Tsohon ministan sufuri, Mu’azu Jaji Sambo, ya bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027
  • Sambo ya bukaci ’yan Najeriya su bai wa Tinubu wa’adi na biyu domin ƙarfafa sauye-sauyen tattalin arziki da manufofin ci gaban gwamnatinsa
  • Jigon APC ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta samu gagarumar nasara a babban zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon ministan sufuri, Alhaji Mu’azu Jaji Sambo, ya bayyana goyon bayansa ga yunƙurin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman wa'di na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Sambo ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC za ta taka rawar gani a babban zaɓe mai zuwa kuma za ta samu nasara.

Bola Tinubu.
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Roc da ke Abuja Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Leadership ta ruwaito cewa Sambo, wanda ya kasance mai kula da ayyukan kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima a jihar Taraba a lokacin zaɓen 2023, ya bayyana hakan ne a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya sake neman alfarmar yan Najeriya yayin kamfen a Kaduna

An bukaci yan Najeriya su zabi Tinubu

Tsohon ministan ya bukaci ’yan Najeriya su bai wa Tinubu wa’adi na biyu domin ƙarfafa sauye-sauyen tattalin arziki da manufofin ci gaban gwamnatinsa.

Goyon bayan na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa da shawarwari gabanin babban zaɓen 2027 ke ƙara ƙarfi.

Ana sa ran ayyukan shugaban ƙasar, manufofinsa na tattalin arziki da kuma damar sake zaɓensa za su kasance cikin manyan batutuwan muhawarar siyasa.

Abubuwan da za su ba Tinubu nasara

Alhaji Sambo ya bayyana kwarin gwiwar cewa sauye-sauyen tattalin arziki, ƙarin zuba jari a ababen more rayuwa, za su samar wa ’yan Najeriya alfanun da za su daɗe ana amfana da su.

“Ba mu yi biris da ra’ayoyin talakawa da kuma yadda tsadar rayuwa ke ƙaruwa ba. Sai dai mun yi imanin cewa sadaukarwar da ake yi a yau ta zama dole domin samun daidaiton tattalin arziki da kuɗi mai ɗorewa,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Bukatar da Shettima ya nema wajen 'yan Arewa kan tazarcen Tinubu

Ya bukaci ’yan Najeriya su ba Tinubu damar ƙarfafa shirin farfaɗo da tattalin arzikin gwamnatinsa ta hanyar sake zaɓensa wa’adi na biyu, yana mai cewa ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen zai inganta makomar tattalin arzikin ƙasar.

“Muna tabbatar wa ’yan Najeriya cewa al’amura za su inganta. Na yi imani da cewa sauye-sauyen, tare da wasu matakan tallafi, ciki har da ayyukan more rayuwa, za su haifar da daidaiton tattalin arziki da wadata ga al’umma a dogon lokaci,” in ji shi.

Sambo ya ba gwamnatin Tinubu shawara

Jigon na APC, wanda ya taɓa neman takarar gwamnan Taraba a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da ya gabata, ya kuma yi kira da a inganta yadda ake sanar da jama’a manufofin gwamnatin a matakin ƙananan hukumomi da al’ummomi.

Alhaji Mu’azu Jaji Sambo.
Tsohon ministan sufuri, Alhaji Mu’azu Jaji Sambo Hoto: Mu’azu Jaji Sambo
Source: Facebook

Ya jaddada cewa jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki a siyasa suna bukatar ƙara ƙoƙari wajen bayyana wa talakawa amfanin sauye-sauyen tattalin arzikin, na yanzu da kuma na dogon lokaci.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya da masu ruwa da tsaki a siyasa da su goyi bayan shirin ci gaban shugaban ƙasar, yana mai cewa:

“Na yi imanin cewa lokaci ya yi da ya kamata dukkanmu mu haɗa hannu da Shugaba Tinubu domin gina ƙasarmu.”

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun yi magana da murya 1 kan sake zaben Tinubu a zaɓen 2027

Ministan ya yaba taron Kaduna

Kun ji cewa Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce ’yan Najeriya na son Tinubu, yana mai kira gare su su yi watsi da labaran kafafen sada zumunta.

Ya bayyana yawan mutanen da suka halarci gangamin Kduna a matsayin alamar karɓuwar shugaban ƙasa a tsakanin ’yan Najeriya, musamman magoya bayan da suka yi imani da manufofinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262