Fusatattun Matasa Sun Farmaki Dan Majalisar Tarayya na APC a Kano da Duwatsu

Fusatattun Matasa Sun Farmaki Dan Majalisar Tarayya na APC a Kano da Duwatsu

  • Wasu matasa sun kai hari kan ayarin ɗan majalisar APC mai wakiltar Gezawa/Gabasawa a Kano, Muhammad Chiroma Nalabara
  • Masu zanga-zangar sun bayyana fushinsu kan zargin gazawar ɗan majalisar wajen magance matsalolin al’umma da samar da muhimman abubuwan more rayuwa a yankin
  • Har yanzu ɗan majalisar da rundunar ’yan sandan Kano ba su fitar da sanarwa kan lamarin ba, kuma ba a san ko an jikkata wani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - An ruwaito cewa wasu fusatattun matasa sun kai hari kan ayarin ɗan majalisar jam’iyyar APC, Muhammad Chiroma Nalabara.

Dan majalisar shi ne mai wakiltar mazaɓar Gezawa/Gabasawa ta tarayya a Majalisar Wakilai, yayin wata ziyara da ta shafi kamfen a Garuruwa, ƙaramar hukumar Gabasawa da ke Kano, ranar Asabar.

An farmaki dan majalisa a Kano
Taswirar jihar Kano da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Matasa sun farmaki dan majalisar tarayya a Kano

Kara karanta wannan

Siyasa na ɗaukar zafi, ƴan daba sun farmaki ɗan takarar majalisa, an rasa rai

Shafin Bakatsine da ya ke yawan kawo rahotanni kan tsaro ya tabbatar da faruwar hakan inda ya wallafa bidiyon a shafin X.

Majiyoyi sun ce matasan sun riƙa jifan ayarin motocin da wasu abubuwa domin nuna adawa da abin da suka bayyana a matsayin gazawar ɗan majalisar wajen biyan buƙatun al’ummarsu, duk da tsawon lokacin da ya shafe a kan muƙaminsa.

Wasu bidiyoyi da suka yaɗu a kafafen sada zumunta sun nuna matasa da dama suna tafiya a kan wata babbar hanya, inda wasu daga cikinsu ke riƙe da dogayen sandunan itace da kulake.

An kuma ji masu zanga-zangar suna rera wasu kalamai cikin yarensu na gida, inda suke bayyana takaicinsu kan zargin rashin ci gaba da kuma rashin muhimman abubuwan more rayuwa a yankinsu.

AN farmaki dan majalisa daga Kano
Fusatattun matasa da suka kai hari kan ayarin motocin dan majalisar tarayya daga Kano, Muhammad Chiroma Nalabara. Hoto: @DanKatsina50.
Source: Twitter

Yadda matasa suka kai hari kan dan majalisa

A cikin sanarwar, an ce an kai harin ne kan ayarin motocin a lokacin ziyarar da ɗan majalisar ya kai yankin, bidiyon ya nuna matasan suna jifan motocin da wasu abubuwa.

Ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, Nalabara da rundunar ’yan sandan jihar Kano ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun farmaki ayarin ɗan takarar jam'iyyar su Kwankwaso, an kashe mutum 1

Haka kuma, har yanzu ba a tabbatar da ko wani ya jikkata ko kuma an kama wasu da ake zargi da hannu a harin ba.

Yawan kai hari da farmaki kan yan siyasa ya zama ruwan dare musamman a wannan kakar zabe ta 2027 da ake gani za ta yi zafi sosai fiye da sauran zabubbuka da suka wuce.

An farmaki dan takarar dan majalisa

Mun ba ku labarin cewa rundunar ’yan sandan Ebonyi ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya, yayin da wasu uku suka jikkata bayan wasu ’yan daba sun kai hari ayarin ɗan takarar NDC.

Ɗan takarar majalisar dokokin jihar, Rollins Offia-Nwali, ya ce maharan sun ƙona motarsa kirar Toyota Hilux, amma shi da tawagarsa sun tsira ba tare da rauni ba.

Offia-Nwali ya yi ta’aziyya ga waɗanda harin ya shafa, tare da gargaɗin matasa kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen cimma muradunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.