Atiku Ya Ce Zai Janye wa Obi Takara idan Aka Cire Kwankwaso daga Mataimaki?

Atiku Ya Ce Zai Janye wa Obi Takara idan Aka Cire Kwankwaso daga Mataimaki?

  • Wasu sun yi ta cewa Atiku Abubakar ya ce zai janyewa Peter Obi takara idan Kwankwaso ya bar kujerar mataimakin shugaban ƙasa
  • Kakakin Atiku, Paul Ibe, ya ce bai kamata a tilasta wa kowane ɗan takara janyewa ba, yayin da ‘yan adawa ke ƙoƙarin cimma matsaya
  • Bincike ya nuna cewa babu hujjar da ta tabbatar da iƙirarin cewa Atiku zai janyewa Obi takara bisa sharadin Kwankwaso ya sauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani saƙo da aka wallafa a kafafen sadarwa ya danganta wani furuci ga Atiku Abubakar kan janye wa Peter Obi.

Rahoton ya nuna cewa wai Atiku ya ce zai janyewa Peter Obi takara idan Rabiu Kwankwaso ya janye daga matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC.

Atiku ya karyata shirin janye wa Obi' takara
Atiku Abubakar, Rabi'u Musa Kwankwaso da Peter Obi. Hoto: Atiku Abubakar, Mr Peter Obi.
Source: Facebook

Oloh Achunike ne ya wallafa wannan iƙirari a wani rukunin Facebook mai suna Nigeria News – Headlines Today.

Kara karanta wannan

Wike ya faɗi abin da zai hana Obi zama shugaban ƙasa, ya tuna mummunan halinsa 1

Abin da ake yaɗawa kan Atiku Abubakar

Saƙon ya ƙunshi wani hoto mai rubutu cewa:

“Zan janyewa Peter Obi takara idan Kwankwaso ya bar matsayin mataimakin shugaban ƙasa, domin ADC ta fitar da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.”

Abu Amir, wani mai amfani da shafin X mai suna @SadiqMaunde, shi ma ya wallafa irin wannan iƙirari a ranar 19 ga Oktoba, tare da saƙon da ke nuna cewa Atiku yana shirin janyewa daga takara domin samar da tikitin haɗin gwiwar Obi da Kwankwaso, wanda ake kira da tikitin “OK."

Waɗannan saƙonni suna nuna cewa Atiku ya amince zai janye burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa bisa wani tsari na musamman da ya shafi Obi da Rabiu Kwankwaso.

An yaɗa karairayi kan Atiku Abubakar
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Kakakin Atiku ya yi bayani

Paul Ibe, kakakin Atiku, ya shaida wa CableCheck a ranar Lahadi cewa bai kamata a tilasta wa kowane ɗan takara janyewa daga takara ba.

Kara karanta wannan

Bayan zargin son Pantami, Wike ya magantu kan taimakon wani dan takara

Ibe ya ce:

“Bai kamata a tilasta wa kowa janyewa daga takara ba. Hakika, ƙungiyar haɗakar ‘yan adawa tana aiki domin tabbatar da cewa ‘yan adawa sun yi amfani da wannan babbar dama ta tarihi da zaɓen 2027 ya samar.
"Tsarin da ƙungiyar haɗakar ta samar zai taimaka wajen buɗe hanyar da ‘yan takarar za su bi domin cimma matsaya tare da amincewa da ita.”

Furucin Ibe ya nuna cewa ana ci gaba da ƙoƙarin samar da matsaya tsakanin jam’iyyun adawa kan ‘yan takararsu.

Sai dai bai tabbatar da iƙirarin da ake yaɗawa ba na cewa Atiku ya yi tayin janyewa domin Obi bisa sharadin Kwankwaso ya bar kujerar mataimakin shugaban ƙasa.

Rahotannin da suka yi bincike ba su tabbatar da iƙirarin cewa Atiku ya ce zai janyewa Obi takara idan Kwankwaso ya bar matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC ba.

Wike ya dura kan Peter Obi

Mun ba ku labarin cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana Peter Obi a matsayin mutum mai rowa, yana mai cewa bai cancanci shugabancin Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Ana zargin yana tare da APC, Kwankwaso ya bada shawara kan sake zaɓen Tinubu a 2027

Wike ya soki Obi kan ɗaukar jakarsa da kansa, yana mai cewa shahararsa a kafafen sada zumunta ba ta tabbatar da ƙwarewar shugabanci ba.

M ehinistan ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu da APC a zaɓen 2027, tare da zargin almundahanar kuɗi a wasu ayyukan gwamnatin Rivers.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.