Kamfen Tinubu: APC Ta Yi Mamakin Ƙarairayin Atiku Wurin Amfani da AI
- Jam’iyyar APC ta zargi Atiku Abubakar da ADC da shirin amfani da bidiyoyin bogi da takardun ƙarya domin ɓata taron kamfen ɗinta a Kaduna
- Kakakin kwamitin kamfen APC, Dele Alake, ya ce an ƙirƙiri wasiƙar bogi da ke zargin gwamnatin Kaduna da kashe naira tiriliyan 2.3 wajen taron
- APC ta yi zargin cewa ana shirin yaɗa tsofaffin bidiyoyi da aka sauya domin nuna rashin amincewar jama’a, tare da kira ga ’yan Najeriya su yi taka-tsantsan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Jam’iyyar APC ta zargi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da yada karairayi game da kamfen dinta a Kaduna.
APC na zargin Atiku da shirya amfani da bidiyoyin bogi da takardun ƙarya domin ɓata taron buɗe kamfen shugaban ƙasa a Kaduna.

Source: Getty Images
Hakan na cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, kakakin kwamitin kamfen shugaban ƙasa na APC, Dele Alake, ya fitar wanda Bayo Onanuga ya wallafa a X.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Jami'an tsaro sun mamaye wuraren da aka liƙa fastoci da allunan tallata Tinubu
Kamfen Kaduna: APC ta yi wa Atiku martani
Alake ya ce sun gano wani shiri da aka tsara domin ɓata taron kamfen ɗin jam’iyyar a Kaduna ranar Asabar, 24 ga Oktoba, 2026.
A cewar kwamitin, ADC da ɗan takararta na shugaban ƙasa sun kammala shirye-shiryen yaɗa bayanan ƙarya da ruɗani, tare da amfani da labaran bogi, bidiyoyin da aka ƙirƙira ta fasahar AI da takardun jabu domin karkatar da ra’ayin jama’a.
Sanarwar ta ce ana son kai hari kan taron kamfen na Kaduna, Shugaba Bola Tinubu, Gwamna Uba Sani da sauran shugabannin APC.
Kwamitin ya ce an fara amfani da waɗannan dabaru cikin sa’o’i 24 da suka gabata, inda aka yaɗa hoton motar jami’an tsaro da ke sintiri a wani mahadar hanya kusa da allunan tallan kamfen APC a cikin birnin Kaduna.
Kwamitin ya yi zargin cewa Atiku da ADC sun karkatar da labarin, inda suka ce jami’an tsaron suna gadin allunan tallan kamfen APC a Kaduna.

Kara karanta wannan
Atiku ko Tinubu: An raba gardama kan dan takarar da ya fi dacewa ya zama shugaban kasa
Ya ƙara da cewa an yaɗa labarin a wata jaridar ƙasa da kwamitin ya bayyana a matsayin mai adawa da gwamnati da APC.
Sanarwar ta ce, bayan jaridar ta wallafa labarin da kwamitin ya kira na ƙarya kuma wanda aka karkatar, Atiku Abubakar ya raba shi a shafukansa na sada zumunta domin yaɗa shi da kuma jawo hankalin jama’a.
Kwamitin ya ce lamari na biyu shi ne yaɗa wata wasiƙar bogi a intanet, wadda aka yi iƙirarin cewa Gwamna Uba Sani ne ya rubuta ta zuwa ga babban daraktan kwamitin kamfen APC, Sanata Abdulaziz Yari.
A cewar kwamitin, wasiƙar ta yi zargin cewa gwamnatin jihar Kaduna ta saki naira tiriliyan 2.3 domin ɗaukar nauyin taron kamfen APC.
Sai dai kwamitin ya yi watsi da wannan iƙirari, yana mai cewa zargin ba shi da tushe kuma ya saɓa wa hankali.
Sanarwar ta ce:
“Har yanzu muna mamakin yadda wani zai ƙirƙiro wannan ƙarya marar tushe wadda ta saɓa wa hankali da tunani na yau da kullum. Nawa ne jimillar kuɗaɗen shigar Kaduna ko kowace jiha a shekara har jiha ta kashe naira tiriliyan 2.3 wajen gudanar da taro?”

Kara karanta wannan
2027: Ana zargin wasu ƙusoshin APC sun fito da kudi don ruguza shirin hadewar yan adawa
Kwamitin ya ƙara da cewa kuɗin da Atiku da mutanensa ke yaɗawa a intanet sun fi kasafin kuɗin Kaduna na tsawon shekaru uku.
Sanarwar ta bayyana cewa haɗaɗɗun kasafin kuɗin Kaduna na shekarar 2024, naira biliyan 458.271; na 2025, naira biliyan 790.439; da na 2026, naira biliyan 985.9, har yanzu ba su kai naira tiriliyan 2.3 ba.
APC ta yi gargaɗi kan bidiyoyin bogi
Kwamitin ya yi gargaɗin cewa waɗannan lamura biyu wani ɓangare ne kawai na babban shirin da ake zargin ADC da Atiku suna aiwatarwa.
Ya ce mutanen da ke aiki da ADC da Atiku sun shirya yaɗa tsofaffin bidiyoyi da aka sauya da kuma bidiyoyin bogi yayin da taron kamfen ke gudana, domin nuna kamar jama’a ba su amince da taron ba.
Kwamitin ya kuma zargi Atiku da ADC da yin duk mai yiwuwa, ko da kuwa abin kunya ne, domin cimma burinsu na karɓe mulki.
A ƙarshe, kwamitin kamfen APC ya yi kira ga ’yan Najeriya da su kasance masu lura da abubuwan da ake yaɗawa, tare da ƙin yarda da dabarun da ya ce ana amfani da su wajen yaudarar jama’a.
Karin bayani na tafe....
Asali: Legit.ng