Yadda 'Yunwa' Za Ta Ruguza Lissafin Tinubu a Zaben Shugaban Kasa na 2027

Yadda 'Yunwa' Za Ta Ruguza Lissafin Tinubu a Zaben Shugaban Kasa na 2027

  • Jigon ADC, Dele Momodu, ya ce babu dabarar siyasa da za ta taimaka wa Shugaba Bola Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027
  • Momodu ya ce ’yan Najeriya sun farka, kuma za su iya karɓar kuɗin da aka ba su a lokacin zaɓe amma su zaɓi wanda suke so
  • Fadar shugaban ƙasa ta yi watsi da kalaman Momodu, inda ta ce ’yan adawa na yin suka ba tare da la’akari da nasarorin da aka samu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wani jigo a ADC, Cif Dele Momodu, ya bayyana cewa babu wata dabarar siyasa da za ta ceci Shugaba Bola Tinubu daga shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Dan siyasar ya bayyana cewa yunwa da matsin rayuwa da ’yan Najeriya ke fuskanta za su yi tasiri sosai wajen tantance sakamakon zaɓen da ke tafe.

Kara karanta wannan

An samu matsala: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya cire kansa daga shirin su Atiku a 2027

Dele Momodu.
Jigo a jam'iyyar adawa ta ADC kuma fitaccen dan jarida, Dele Momodu Hoto: Dele Momodu
Source: Facebook

Momodu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, wanda Seun Okinbaloye ke gabatarwa.

A cewarsa, matsin tattalin arziki ya zama abin da ya haɗa ’yan Najeriya daga dukkan yankuna da ƙabilu, kuma babu adadin kuɗi ko dabarar siyasa da za ta iya shawo kan matsalar.

“Abin da ya haɗa kowa a yanzu shi ne yunwar da ake fama da ita a ƙasar nan. Babu wata dabarar siyasa da za ta iya kayar da yunwa. Yarabawa na shan wahala, Hausawa na shan wahala, Inyamurai na shan wahala, kowa na shan wahala,” in ji shi.

Momodu ya soki dabarun Tinubu

Momodu ya ce Tinubu ba zai iya sayen dukkan ’yan Najeriya da kuɗi ba, duk da cewa a baya ya yi nasarar amfani da kuɗi wajen gudanar da harkokin siyasa a Jihar Legas.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An gano masu shirya kai farmaki kan matasan da za su y aikin zaɓen 2027

“Tinubu yana ganin zai iya sayen dukkan Najeriya, amma a ra’ayina, idan har ya iya sayen jama'ar Legas, ina shakkar ko zai iya amfani da kuɗi wajen sayen dukkan yan Najeriya,” in ji Momodu.

Ya ce ’yan Najeriya sun ƙara wayewa a harkokin siyasa, kuma za su karɓi duk kuɗin da aka ba su a lokacin zaɓe, amma daga ƙarshe su zaɓi wanda suka ga dama bisa lamirinsu.

Momodu.
Dan jarida kuma jigon ADC, Dele Momodu tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Dele Momodu
Source: Twitter

Ya kawo zaɓen gwamnan Jihar Osun a matsayin misali, inda ya ce duk da zargin kashe kuɗi masu yawa a lokacin zaɓen, jama’a sun zaɓi Gwamna Ademola Adeleke.

Momodu ya kuma tuna cewa Tinubu ya sha kaye a Jihar Legas a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda ɗan takarar LP, Peter Obi, ya samu nasara a jihar.

Ya ce hakan ya nuna cewa kasancewa shugaban ƙasa ko samun ƙarfin kuɗi ba ya tabbatar da nasara a zaɓe, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Ya dage cewa Tinubu ba zai lashe zaɓen 2027 ba, yana mai cewa da yawa daga cikin ’yan Najeriya ba za su iya tunanin yi wa gwamnatin shugaban ƙasar wa’adi na biyu ba.

Kara karanta wannan

Tinubu na da abin da zai fada wa yan Najeriya su zaɓe shi a 2027? Baba Ahmed ya yi magana

Matsalar da yan adawa ke fuskanta

Kun ji cewa shugabannin ’yan adawar Najeriya na ci gaba da tattaunawa domin samar da haɗin kai da zai iya ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu.

Yayin da ake ci gaba da shawarwari tsakanin jam’iyyun adawa, burin samun kujerar shugaban ƙasa, saɓanin akidu da rashin sanin yadda za a zaɓi ɗan takara na haɗin gwiwa na barazana ga nasarar tattaunawar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262