Babbar Magana: Tinubu Ya Yi Yabo ga ADC, Ya Fadi Alherin da Ta Yi Masa
- Shugaba Bola Tinubu ya gode wa ADC cikin raha, yana mai cewa jam’iyyar ta taimaka wajen hana shi yin barci
- Tinubu ya yaba da tsarin CityBoy Movement, yana mai cewa ƙungiyar ta gina hanyar sadarwa mai faɗi maimakon tara jama’a a tarukan siyasa kawai
- Shugaban ya jinjina wa cibiyar kiran wayar ƙungiyar da shirin CityBoy Care saboda hulɗarsu da matasa da sauraron buƙatun al’umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC) habaici.
Shugaba Bola Tinubu ya gode wa babbar jam'iyyar adawar bisa abin da ya ce ta yi na hana shi yin barci.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce Tinubu ya yi wannan furuci ne yayin wani taron girmamawa da magoya bayan CityBoy Movement da ƙungiyar Relax Tinubu Is Fixing Nigeria (RTIFN) a Abuja ranar Litinin, 19 ga watan Oktoban 2026.
Tinubu ya yi wa ADC habaici gabanin zaɓen 2027
A yayin taron, Tinubu ya ce:
“Wasu mutane sun yi tunanin cewa zuwa yanzu zan gaji kuma barci zai ɗauke ni, tun da na zo nan a kan lokaci. Na gode, ADC.”
Wannan furuci ya zo ne yayin da Tinubu ke shirin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yake takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin ADC.
Shugaban ya bayyana cewa ƙoƙarin ƙungiyoyin na tattara goyon bayan jama’a tun daga tushe zai ba shi damar hutawa cikin kwanciyar hankali, yana mai nuna amincewarsa da faɗin tasirinsu da tsarin gudanarwarsu.
Tinubu ya yaba da tsarin CityBoy Movement
A cewar Tinubu, CityBoy Movement ta kawo sabon salo a harkokin siyasar Najeriya, ta hanyar gina hanyar sadarwa da ta wuce tara jama’a a tarukan siyasa.
“Ku na CityBoy Movement, kun yi wani sabon abu a siyasar Najeriya. Ba tara mutane kawai kuka yi ba; kun gina tsari mai miliyoyin mambobi na gaske waɗanda za a iya tantancewa.” In ji shi.
Tinubu ya kuma yi magana kan kasancewar ƙungiyar a faɗin ƙasar, yana mai cewa tsarinta ya kai matakin jihohi, ƙananan hukumomi, unguwanni da rumfunan zaɓe.
“Kuna da wakilci a kowace jiha, kowace ƙaramar hukuma, kowace unguwa, har zuwa rumfunan zaɓe.” In ji shi.
Shugaban ya yaba da ayyukan kungiyar
Tinubu ya kuma jinjina wa yadda ƙungiyar ke hulɗa da matasan Najeriya ta hanyar cibiyar kiran wayarta da shirin tallafa wa al’umma mai suna CityBoy Care.
“Kun kai ayyukanku har matakin ƙasa; kuna da cibiyar kira da ke magana da matasan Najeriya a kullum, tare da sauraron buƙatun al’ummominsu. CityBoy Care kuma na haɗuwa da mambobi a wuraren da suke zaune.” In ji shi.
Shugaban ya bayyana ayyukan ƙungiyar a matsayin alamar ingantaccen tsarin hulɗa da jama’a tun daga tushe, maimakon tattara jama’a don neman farin jini kawai.
Ya ce ƙoƙarin ƙungiyar na isa ga al’umma da sauraron buƙatunsu ya ƙara masa kwarin gwiwa game da shirinta na tattara goyon bayan jama’a gabanin zaɓe mai zuwa.
Tinubu ya ce kasancewar ƙungiyar na aiki a matakin al’umma zai ba shi damar komawa gida ya “yi barci cikin kwanciyar hankali.”

Kara karanta wannan
Yari: Idan Buhari ya gaza magance matsalar tsaron Najeriya, me ku ke tunani daga Tinubu?

Source: Twitter
Tinubu ba zai dawo da tallafin fetur ba
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sake bayyana matsayarsa kan dawo da tallafin man fetur.
Shugaba Tinubu ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta dawo da tsarin tallafin man fetur ba, yana mai cewa matakin da ya ɗauka ya zama dole domin gyara tattalin arzikin ƙasar.
Asali: Legit.ng

