2023: ‘Dan Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya daurewa Gwamnan APC gindi ya shiga takara

2023: ‘Dan Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya daurewa Gwamnan APC gindi ya shiga takara

- Olujonwo Obasanjo ya na goyon bayan takarar Yahaya Bello a zabe mai zuwa

- ‘Dan tsohon shugaban kasar ya na sha’awar matasa su karbi mulkin Najeriya

- Obasanjo ya ce an dade ana hana matasa mukami duk da dinbin adadin na su

A daidai lokacin da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ke bayyana muradinsa na takarar shugaban kasa a 2023, ya samu karin karfin gwiwa.

Olujonwo Obasanjo wanda ‘da ne wajen tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, wanda ya yi mulki sau biyu a 1976 da 1999, ya goyi bayan APC a zaben 2019.

Jaridar Vanguard ta ce Mista Olujonwo Obasanjo ya shiga sahun masu goyon bayan Yahaya Bello ya yi takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2003.

KU KARANTA: Gaskiya da amanar APC za su sa ta ci zabe a 2023 - Badaru

Obasanjo ya na ganin burin gwamnan na jihar Kogi na neman babbar kujerar kasar nan ya zo a daidai.

Olujonwo Obasanjo wanda kwanakin baya ya yi ta samun matsala da mai dakinsa, ya kira zuwan Bello da sa ran samun nasara, ya kira shi ya tashi-tsaye.

Matashin da ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya kai wa gwamnan ziyara a gidansa da ke garin Abuja a jiya, ya fada masa cewa matasa su na tare da shi.

Jonwo Obasanjo yake cewa an dade ana danne matasa a Najeriya duk da adadinsu da kuma irin gudumuwar da su ke bada wa a wajen siyasar kasar nan.

KU KARANTA: Ministan jamhuriyya ta biyu kuma tsohon Sanatan Najeriya ya mutu

2023: ‘Dan Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya daurewa Gwamnan APC gindi ya shiga takara
Olujonwo Obasanjo tare da Shugaban kasa Buhari
Asali: Facebook

A cewarsa, babu abin shakka game da kishin kasa da kokarin ‘yan shekara 35 zuwa 45 kamar yadda aka gani a baya a lokacin irinsu Janar Muhammadu Buhari, T. Y. Danjuma, Yakubu Gowon da kuma mahaifinsa, Olusegun Obasanjo.

Idan Bello ya samu mulki, matasa masu shekara 27 zuwa 30 za su iya zama Ministocin tarayya.

A karshe ya yaba wa kokarin Bello wajen gina abubuwa more rayuwa da inganta tsaro, sannan yi kira ga gwamnan ya tsaya tsayin-daka wajen neman takarar.

Dazu an ji cewa tsohon babban hafsun sojojin kasa, Janar Oyeabo Ihejirika ya shiga jam'iyyar APC.

Darektan watsa labarai na gwamnan Yobe kuma shugaban kwamitin riko na APC, Alhaji Mamman Mohammed ne ya bada wannan sanarwar da rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng