Kotu Ta Yanke Hukunci kan Bukatar Tsige Dan Majalisar Tarayya daga Jihar Kaduna

Kotu Ta Yanke Hukunci kan Bukatar Tsige Dan Majalisar Tarayya daga Jihar Kaduna

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da ke neman tsige ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Igabi a Jihar Kaduna, Hussaini Jallo
  • Jam’iyyar PDP ce ta shigar da ƙarar bayan zargin cewa Jallo ya fice daga cikinta zuwa jam’iyyar APC mai mulki
  • Mai shari’a James Omotosho ya ce PDP ta gaza gabatar da sahihiyar hujjar da za ta tabbatar da cewa Jallo ya sauya sheƙa zuwa APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da ke neman a cire ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Igabi a Jihar Kaduna, Hon. Hussaini Jallo, daga kujerarsa.

An nemi kotun ta sauke dan Majalisar tarayya ne saboda zargin ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Matsala ta faru: Cutar Ebola ta dawo Najeriya, an ɗauki tsauraran matakai

Hussaini Jallo.
Dan Majalisar wakilai mai wakiltar Igabi daga Kadun, Hon. Hussaini Jallo yayin zaman Majalisa a Abuja Hoto: Muhd Rabiu Nasir
Source: Facebook

Daily Trust ta ce a hukuncin da ya yanke a ranar Talata, Mai shari’a James Omotosho ya ce PDP, wadda ta shigar da ƙarar, ta gaza gabatar da wata sahihiyar hujja da za ta tabbatar da cewa sauya sheƙar Jallo zuwa APC ba ta dace da doka ba.

PDP ta nemi a tsige dan Majalisa

PDP ta shigar da ƙarar tare da haɗa Jallo, Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a matsayin waɗanda ake ƙara na farko, na biyu da na uku.

A cikin takardar ƙarar da ta gyara, jam’iyyar ta nemi kotu ta bayyana cewa, tun da Hon. Jallo ya fice daga PDP, wadda ta tsayar da shi takara kuma a ƙarƙashin inuwarta aka zaɓe shi, ya kamata ya bar kujerarsa nan take.

Abin da Hussaini Jallo ya ce

A cikin rantsuwar amsa ƙarar da ya gabatar, dan Majalisar ya musanta cewa shi tsohon mamban PDP ne, yana mai cewa har yanzu cikakken mamba ne na jam’iyyar kuma yana riƙe da katin zama mamba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso na fuskantar matsala a Kano, yan takara 5 sun dura kan 'yan Kwankwasiyya

Ya bayyana cewa har yanzu yana biyayya da amana ga jam’iyyar, kuma bai miƙa ko gabatar da wata takardar murabus ko ta sauya sheƙa daga PDP a mazaɓar zaɓensa ba.

A nasa ɓangaren, Tajudeen Abbas, ya bayyana a cikin rantsuwar amsa ƙarar cewa, sabanin zargin PDP, bai taɓa sanarwa ko karanta wata takarda a zauren majalisar da ke nuna cewa Jallo ya fice daga PDP zuwa APC ba.

Haka kuma, INEC ta bayyana a cikin rantsuwar amsa ƙarar cewa PDP na fama da rikicin cikin gida, wanda ya haifar da samuwar shugabannin jam’iyya guda biyu masu gudanar da ayyukansu.

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita yayin zaman shari'a a kotu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hukuncin da kotu ta yanke

A lokacin yanke hukunci, Mai shari’a Omotosho ya amince da hujjar PDP cewa tana da haƙƙin shigar da ƙarar, kuma wajibi ne a haɗa ta cikin shari’ar, sabanin abin da Jallo ya yi iƙirari, cewar rahoton Leadership.

Sai dai alkalin ya ce tun da PDP ta gaza tabbatar da cewa Jallo, wanda ake ƙara na farko, ya fice daga cikinta zuwa APC, babu wata hujja da za ta tallafa wa buƙatun da jam’iyyar ta gabatar a gaban kotun.

Kara karanta wannan

Yari: Idan Buhari ya gaza magance matsalar tsaron Najeriya, me ku ke tunani daga Tinubu?

Kotu ta zabukan fitar da gwani 2

Kun ji cewa kotunan tarayya da ke Gombe da Jos sun soke zaɓen fitar da ’yan takarar ADC da APC a wasu mazabun tarayya, tare da umartar gudanar da sabon zaɓe.

Kotunan sun yanke wannan hukunci ne bayan ƙalubalantar yadda aka gudanar da zaɓen fitar da ’yan takarar jam’iyyun gabanin babban zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262