Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci kan Bukatar bada Belin Malam Nasir El Rufai

Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci kan Bukatar bada Belin Malam Nasir El Rufai

  • Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Kaduna ta yi watsi da bukatar ba da belon tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai
  • Kotun ta ce El-Rufai bai gabatar da sababbin hujjoji ko wasu dalilai na musamman da za su sa a sauya hukuncin kotun ƙasa ba
  • An tsara fara shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan a ranar 12 ga Oktoba, 2026, yayin da ya shafe kusan watanni takwas a tsare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Kaduna ta yi watsi da ƙarar da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya shigar domin ƙalubalantar hukuncin Babbar Kotun Jihar Kaduna na hana shi beli.

A hukuncin da ta yanke kan ƙara mai lamba CA/K/254C/2026, kotun ta tabbatar da hukuncin kotun ƙasa wanda ya ahana ba fa belin Malam Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

Rigima: Tambuwal ya maka gwamnatin Sokoto kara gaban kotu

El Rufai.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Facebook

A rahoton Channels tv, Kotun daukaka kara ta bayyana cewa alƙalin da ya jagoranci shari’ar a babbar kotun jiha ya yi amfani da ikonsa na shari’a yadda ya kamata ba tare da tauye adalci ba.

Kotu ta sake hana belin El-Rufai

A cikin hukuncin da alƙalai uku suka yanke baki ɗaya, kotun ta ce El-Rufai bai gabatar da sababbin hujjoji ko wasu yanayi na musamman da za su sa ta sa baki wajen sauya hukuncin kotun ƙasa na hana shi beli ba.

Bisa ga sahihin kwafin hukuncin kotun, Mai Shari’a Onyekachi Aja Otisi ne ya gabatar da hukuncin, inda ya tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Jihar Kaduna na ranar 10 ga Yuni, 2026, wanda ya ƙi amincewa da buƙatar belin El-Rufai karo na biyu.

Kotun ta kuma yi watsi da ƙarin bayani da ɓangaren mai ƙara ya shigar a ranar 29 ga Satumba, tana mai cewa ba a gabatar da shi bisa ƙa’idojin shari’a ba.

Kara karanta wannan

Shari'ar El Rufa'i ta kara zafi, an tabo maganar kwace kadarorinsa a kotu

Dalilin hana Belin El-Rufai

Haka kuma, kotun ta yanke hukunci kan batun da aka gabatar mata domin tantancewa a kan El-Rufai, tare da amincewa bayanan GwamnatinnTarayyar Najeriya.

Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta bayyana cewa ba za ta tsoma baki cikin binciken hujjojin da kotun shari’a ta yi ba, matuƙar ba a nuna cewa hukuncin ya kauce wa gaskiya ko hujjojin da aka gabatar ba.

Kotu.
Gudumar da ake amfani da ita a zaman kotu a Najeriya Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Saboda haka, ta yi watsi da ƙarar El-Rufai ya daukaka domin samun beli, tana mai cewa ba ta da hujjar da za ta sa a amince da ita.

An tsara fara sauraron shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan a ranar 12 ga Oktoba, 2026, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kotu ta yi watsi da bukatar El-Rufai

A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da ya shigar domin hana ICPC ƙwace kadarorinsa.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta ce ƙarar ta saba tsarin shari’a, kasancewar El-Rufai ya shigar da makamantanta a wasu kotuna a kasar nan

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262