Yari: Idan Buhari Ya Gaza Magance Matsalar Tsaron Najeriya, Me Kuke Tunani daga Tinubu?
- Sanata Abdulaziz Yari ya ce bai kamata a ɗora wa Shugaba Bola Tinubu laifin matsalar rashin tsaro da ke addabar ƙasar gaba ɗaya ba
- Ya ce tsohon Shugaba, Muhammadu Buhari, wanda janar ne mai ritaya, ya yi iya ƙoƙarinsa amma bai samu nasarar kawo ƙarshensa gaba ɗaya ba
- Abdulazizi Yari ya ce kwamitin yaƙin neman zaɓen zai yi aiki tare da dukkan mutanen da ƙungiyoyin da suka himmatu wajen tabbatar da sake zaɓen Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi, Nigeria - Daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce ba za a ɗora wa Shugaba Bola Tinubu laifin matsalar rashin tsaro da ta addabi ƙasar gaba ɗaya ba.
Sanata Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana haka ne yayin da yake magana a ranar Litinin, 19 ga wwtan Oktoba, 2027 a ziyarar da ya kai jihar Kebbi.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: An ji yadda Buhari ya nuna akwai matsala idan Tinubu ya karbi mulki a 2023

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa a wannan ziyara ya gana da Gwamna Nasir Idris, sarakunan gargajiya da sauran shugabannin jam’iyyar a Birnin Kebbi.
Ssnata Yari ya ce tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, wanda janar ne mai ritaya, ya yi iya ƙoƙarinsa amma bai iya kawo ƙarshen rashin tsaro gaba ɗaya ba.
Sanata Yari ya yaba wa jiga-jigan APC
Ya yaba wa gwamnan da sauran shugabannin APC bisa ƙoƙarin da suke yi na tattara goyon baya ga APC, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa haɗin kansu zai tabbatar da nasarar Tinubu da sauran ’yan takarar APC a zaɓen 2027.
Abdulazizi Yari ya ce kwamitin yaƙin neman zaɓen zai yi aiki tare da dukkan mutanen da ƙungiyoyin da suka himmatu wajen tabbatar da sake zaɓen Tinubu, ba tare da la’akari da matsayinsu ba, domin cimma manufofin jam’iyyar.
Ya bayyana kwarin gwiwarsa kan damar da APC ke da ita ta samun nasara a Kebbi, yana mai cewa goyon bayan da ya gani yayin ziyararsa jihar ya ƙara masa ƙarfin gwiwa.
Yari ya yi magana kan rashin tsaro
Dangane da rashin tsaro, Yari ya amince da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, amma ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu na ƙoƙarin magance matsalar.
Ya tuna cewa tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, wanda janar ne mai ritaya a rundunar soji, shi ma ya yi ƙoƙarin magance rashin tsaro a lokacin mulkinsa, duk da cewa ba a kawar da matsalar gaba ɗaya ba.
“Idan janar mai ritaya ya yi iya ƙoƙarinsa amma bai iya kawo ƙarshen rashin tsaro gaba ɗaya ba, me kuke tsammani daga Shugaba Tinubu wanda ba janar ba ne?
"Duk da haka, shugaban ƙasa ya yi iyakar ƙoƙarinsa wajen magance matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta,” in ji shi.

Source: Facebook
Yari ya kuma buƙaci ’yan Najeriya su yi tunani kan dangantakarsu da Allah, yana mai cewa magance rashin tsaro na buƙatar haɗin kan al’umma tare da ƙoƙarin gwamnati.
Sanata Yari ya fadi shirin APC
Kun ji cewa Sanata Abdulaziz Yari ya yi magana kan shirin da suke suke domin tallata Tinubu ga talakawa da shugabanni gabanin zaben shugaban kasa na 2027.
Ya bayyana cewa alamu sun nuna cewa shugaban kasa Bola Tinubu ne zai yi nasara saboda yadda yake da mutane a Kudu da Arewa.
Asali: Legit.ng
