Rigima Ta Kara Zafi, An Dura kan Magoya bayan Atiku bayan Sun Taba Kwankwaso

Rigima Ta Kara Zafi, An Dura kan Magoya bayan Atiku bayan Sun Taba Kwankwaso

  • Mataimakin darakta janar na OK Movement a Arewa, Prince Abubakar Suleiman, ya gargadi magoya bayan Atiku Abubakar kan Sanata Rabiu Kwankwaso
  • Suleiman ya ce magoya bayan Atiku sun mayar da zargin Kwankwaso al’ada a duk lokacin da rikici ya taso a jam’iyyar ADC
  • Ya kuma bukaci ’yan Najeriya su mara wa tikitin Obi-Kwankwaso baya, yana mai bayyana shi a matsayin mafi kyau a tarihin ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Mataimakin darakta janar na Obi-Kwankwaso Movement a Arewa, Prince Abubakar Suleiman, ya tsoma baki kan rikicin da ya taso tsakanin magoya bayan Atiku Abubakar da Sanata Rabiu Kwankwaso.

Abubakar ya yi kira ga magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Alhaji Atiku Abubakar, da su fuskanci matsalolin cikin gida na jam’iyyarsu, su kuma daina jawo Kwankwaso cikin rikicinsu.

Kara karanta wannan

Hadimin Davido ya saba da shi kan Tinubu, ya fadi alherin mulkin dan Arewa

Kwankwaso.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Ya yi wannan kiran ne a Abuja jiya, bayan wani taro da ya gudanar da masu ruwa da tsaki na OK Movement, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

An gargadi magoya bayan Atiku

Abubakar Suleiman ya ce magoya bayan Atiku sun mayar da jawo Sanata Kwankwaso, mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, cikin duk wata matsala da ta dabaibaye ADC tamkar al’ada.

A cewarsa, Kwankwaso ya mayar da hankali kan nauyin da ke kansa, don haka bai kamata a mayar da shi babban abin zargi kan rikicin cikin gida na ADC ba.

Mataimakin DG ya ce:

“Ya kamata magoya bayan Atiku su cire Kwankwaso daga matsalolinsu, su kyale shi. Su fuskanci matsalolinsu maimakon ɗora laifi kan mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC.”

OK Movement ta tsaya kan manufofi

Abubakar ya bayyana cewa Obi-Kwankwaso Movement na nan daram kan siyasar da ta ginu bisa batutuwa da manufofi, kuma ba za ta bari yunƙurin ɓata wa Kwankwaso suna ya karkatar da hankalinsa daga wannan hanya ba.

Kara karanta wannan

Ana zargin Kwankwaso na taimakon Tinubu ya zarce sabdao wasu dalilai

Ya ƙara da cewa Kwankwaso ya taka rawar gani a siyasar Najeriya, kuma har yanzu yana samun gagarumin goyon baya a faɗin ƙasar saboda tarihin ayyukansa.

Ya jaddada cewa babu yawan hare-haren da ake kai mass kafafen yaɗa labarai da zai iya rage muhimmancinsa a siyasar ƙasar nan.

Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Facebook

Yabo ga yan ƙungiyar Ok Movement

Abubakar Suleiman ya kuma yaba wa mambobin OK Movement a faɗin ƙasar bisa jajircewarsu da sadaukarwarsu, musamman darakta janar na ƙasa na Obi-Kwankwaso OK Movement, John Ughulu.

Daga ƙarshe, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su goyi bayan tikitin Obi-Kwankwaso, yana mai bayyana shi a matsayin mafi kyau a tarihin Najeriya.

Kwankwaso ya maida martani ga ADC

Kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa NDC ba za ta janye wa Peter Obi takara domin goyon bayan ADC ba.

Kwankwaso ya yi zargin cewa ADC na ƙoƙarin yaudarar magoya bayan NDC ta hanyar nuna cewa jam’iyyar na aiki ne da jam’iyyar APC mai mulki.

Ya ce babu wani dalili da zai sa NDC ta janye wa ADC ko wata jam’iyya takara, yana mai jaddada cewa tikitin OK na da ƙwarewa da ƙarfin da ake buƙata domin jagorantar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262