Hadimin Davido Ya Saba da Shi Kan Tinubu, Ya Fadi Alherin Mulkin Dan Arewa
- Wani hadimin mawaki Davido da ake kira Israel DMW ya yi magana game da zaben 2027 tsakanin Bola Tinubu da yan adawa.
- Israel wanda manajan harkokin sufuri na mawaki Davido ne ya nuna goyon bayansa ga Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Ya bayyana cewa mulkin ɗan Arewa ya fi dacewa, tare da sukar kwangilar Naira tiriliyan 15 da aka bai wa mutum guda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lagos - Israel ‘DMW’ Afeare, manajan harkokin sufuri na shahararren mawaki David Adeleke, wanda aka fi sani da mawaki Davido, ya yi magana kan zaben 2027.
Israel DMW ya bayyana goyon bayansa ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Source: Twitter
Hakan na cikin wani sako da hadimin Davido din ya wallafa a shafinsa na Instagram domin bayyana ra'ayinsa kan siyasar 2027.
Yadda Davido ya soki APC a baya
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake sukar mawakin sakamakon goyon bayan da kawunsa, Gwamna Ademola Adeleke na Osun, ya nuna wa Shugaba Bola Tinubu.
Daily Trust ta ce Davido, wanda ya yi kamfen sosai domin kawunsa, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Accord, ya yi takun-saka da jam’iyyar APC mai mulki da shugabanninta a lokacin zaɓen da aka gudanar a watan Agusta.
A baya, Davido ya bayyana cewa ba zai taɓa goyon bayan jam’iyyar APC mai mulki ba.
Sai dai makonni bayan sake zaɓen kawunsa, an rantsar da gwamnan Osun a matsayin ɗaya daga cikin masu jagorantar kamfen ɗin sake zaɓen Tinubu, lamarin da ya jawo wa mawaki Davido suka a kafafen sada zumunta.
Abin da ya sa Israel ya zabi dan Arewa
Israel ya nuna goyon bayansa ga Atiku, ɗan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaɓen shugaban ƙasa.
Ya ce:
“A koyaushe, ya fi kyau idan ɗan Arewa ne yake mulki. An ba mutum guda kwangilar Naira tiriliyan 15 shi kaɗai? Zan zaɓi Alhaji Atiku Abubakar.
“Ya kamata INEC ta bai wa ’yan Najeriya damar zaɓen duk wanda suke so ya shugabance su a watan Janairun 2027. Kyakkyawan suna ya fi kuɗi daraja.
“Haka kuma, ya kamata ’yan Najeriya su yi watsi da batun samun ƙuri’u miliyan 2.5 daga jihar Edo. Adams Oshiomhole har yanzu shi ne gwamnan da aka fi so kuma aka fi karɓa a Edo, inda ya yi nasara a dukkan ƙananan hukumomi 18 cikin 18, amma ya kasa samo wa jam’iyyarsa ƙuri’u 500,000.
“Jam’iyyarsa ta kasa samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa a Edo sau biyu.”
Yan Najeriya sun soki Davido kan Tinubu
A baya, an ji cewa wasu ’yan Najeriya sun yi barazanar kaurace wa bikin rawa na Davido da za a yi a watan Disamba a Lagos.
Davido ya sanar da zai gudanar da kide-kide har dare uku a National Theatre da ke Lagos daga 17 zuwa 19 ga Disamba, 2026.
Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun zargi Davido da munafunci, yayin da wasu suka kare shi.
Asali: Legit.ng


