2027: Zargin Yi wa Tinubu Aiki, Kwankwaso Ya Yi wa ADC Martani cikin Fushi

2027: Zargin Yi wa Tinubu Aiki, Kwankwaso Ya Yi wa ADC Martani cikin Fushi

  • Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa NDC ba za ta janye wa Peter Obi takara domin goyon bayan ADC ba
  • Tsohon gwamnan Kano ya buƙaci ADC ta mayar da hankali wajen amsa zarge-zargen da Kashim Shettima ya yi ga Atiku
  • Kwankwaso ya ce APC ta gaza wa ’yan Najeriya, yayin da NDC ke da ingantacciyar mafita da shirin magance matsalolin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi martani mai zafi ga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) kan zarge-zargenta.

Kwankwaso ya ce NDC ba za ta janye wa ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, takara domin goyon bayan jam’iyyar ADC ba.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a shafin X yayin da yake mayar da martani kan zargin da ADC ke yi masu cewa suna yi wa APC aiki.

Kara karanta wannan

Ana zargin Kwankwaso na taimakon Tinubu ya zarce sabdao wasu dalilai

Ya ce maimakon ADC ta mayar da hankali wajen bayyana ƙwarewa, sahihanci da cancantar ɗan takararta ga ’yan Najeriya, ta fi mayar da hankali wajen yaɗa zarge-zarge da yaƙin ɓata suna kan NDC da takararta.

Kwankwaso ya gargadi ADC kan batun janye takara

Kwankwaso ya yi zargin cewa ADC na ƙoƙarin yaudarar magoya bayan NDC ta hanyar nuna cewa jam’iyyar na aiki ne da jam’iyyar APC mai mulki ko kuma za ta janye takararta a minti na ƙarshe domin goyon bayan ɗan takarar ADC.

Ya bayyana cewa babu wani dalili da zai sa NDC ta janye wa ADC ko wata jam’iyya takara, yana mai jaddada cewa tikitin OK na da ƙwarewa da ƙarfin da ake buƙata domin jagorantar Najeriya.

Ya ce:

“Tikitin OK ba ya aiki da sunan APC ko wani ɗan takararta, kuma ba ya wakiltar muradun jam’iyyar ko wani daga cikin ’yan takararta.”

Ya Bukaci ADC Ta Mayar Da Hankali Kan Zargin Shettima

Tsohon gwamnan ya shawarci kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC da ya mayar da hankali wajen amsa zarge-zargen da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi wa ɗan takararta, maimakon kai hare-hare gare shi da Peter Obi.

Kara karanta wannan

'Nadamar da APC za ta yi a ranar zabe': Kwankwaso ya jaddada kwarin guiwarsu

Kwankwaso ya ce NDC na da cikakken kwarin gwiwar cewa tikitinta na da cancanta, ƙwarewa da goyon bayan jama’a a Arewa da Kudu, tare da kyakkyawan tarihin ayyukan da za ta iya gabatarwa ga ’yan Najeriya.

Kwankwaso ya soki gwamnatin APC

Kwankwaso ya bayyana cewa gwamnatin APC ta gaza wajen biyan buƙatun ’yan Najeriya, yana mai cewa ADC ma ba ta bayar da wata mafita mafi kyau ga ƙasar ba.

Ya ce tikitin OK na da niyyar haɗa kan ’yan Najeriya da magance manyan matsalolin ƙasar, musamman tsaro, ilimi, noma, ababen more rayuwa, kiwon lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe, Kwankwaso ya bayyana NDC a matsayin jam’iyyar adawa mafi ƙarfi da cancanta a Najeriya, tare da kira ga magoya bayanta da sauran ’yan ƙasa masu kishin ƙasa da su ci gaba da aiki domin ganin jam’iyyar ta yi nasara.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.