Zargin Obi da Kwankwaso kan Yi wa Tinubu Aiki na Kara Yawa, An Kawo Masu Mafita

Zargin Obi da Kwankwaso kan Yi wa Tinubu Aiki na Kara Yawa, An Kawo Masu Mafita

  • Fiitaccen lauya, Deji Adeyanju ya yi magana kan zargin takarar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a zaben 2027 da ke tafe
  • Lauyan kare hakkin dan Adam ya ce zai yarda ba sa taimaka wa Bola Tinubu idan suka janye, yana zargin sun taimaka masa a zaben 2023
  • Kwankwaso ya ce Peter Obi yana hana Tinubu sukuni saboda farin jininsa, yayin da ya bayyana cewa ya nemi Fulani su matsa wa Atiku ya janye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ana ci gaba da zargin Peter Obi da Rabi'u Kwankwaso kan yi wa Bola Tinubu aiki game da zaben 2027.

Lauyan kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju, ya ba dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso shawara.

Kara karanta wannan

2027: Kwankwaso ya yi maganar makomar tallafin fetur a gwamnatin Peter Obi

An shawarci Obi da Kwankwaso su hakura da takara
Sanata Rabiu Kwankwaso da dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi. Hoto: Mr Peter Obi.
Source: Twitter

Hakan na cikin wani rubutu da wakilin Legit Hausa ya gano wanda ya yi a shafinsa na Facebook a jiya Juma'a 16 ga watan Oktobar 2026.

Shawarar Adeyanju ga Obi da Kwankwaso

Adeyanju ya ba da shawarar matakin da za su dauka domin nuna ba sa aiki don sake zaben Shugaba Bola Tinubu.

Adeyanju ya ce Obi da Kwankwaso su janye daga takarar shugaban kasa idan har ba sa aiki don ganin Tinubu ya sake lashe zaben 2027.

A sakon da ya wallafa, ya rubuta cewa:

“Idan Obi da Kwankwaso suka janye daga takarar, zan yarda cewa ba sa sake yi wa Shugaba Tinubu aiki kamar yadda suka yi a shekarar 2023.”
Lauya ya shawarci Obi da Kwankwaso
Babban lauya kuma mai kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju. Hoto: Adeyanju Deji.
Source: Twitter

Zargin Adeyanju kan Obi da Kwankwaso

A baya-bayan nan, lauyan ya yi zargin cewa Obi da Kwankwaso suna aiki ne domin taimaka wa Tinubu gabanin babban zaben shekarar 2027.

Adeyanju ya yi ikirarin cewa duk wanda ya kada kuri’a ga mutanen biyu, to ya taimaka wa Tinubu ne. Saboda haka, ya bukaci ’yan Najeriya da kada su zabe su.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya sake maganganu kan Atiku, ya tono tsohon tarihi

Sai dai yayin da Adeyanju ke ci gaba da wannan zargi, Kwankwaso ya dage cewa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na NDC, yana hana Tinubu samun kwanciyar hankali.

Kwankwaso ya bayyana cewa Obi, tsohon gwamnan Anambra, yana da farin jini a Kudancin Najeriya, yayin da ake kokarin wayar da kan al’ummar Arewa domin su mara masa baya.

Ya kuma yi ikirarin cewa halayen Obi da irin farin jinin da yake da shi na daga cikin abubuwan da ke damun Tinubu.

A wani labarin kuma, Kwankwaso ya bayyana cewa ya bukaci kungiyoyin Fulani su matsa wa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), domin ya janye daga takarar shugaban kasa.

ADC tana zargin Kwankwaso da taimakon Tinubu

Mun ba ku labarin cewa kwamitin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ya zargi Rabiu Musa Kwankwaso da ƙoƙarin taimaka wa.

Shugaba Bola Tinubu Kakakin kwamitin kamfen din ADC, Kola Ologbondiyan, ya bayyana kiran Kwankwaso ga Atiku a matsayin abin da bai dace ba.

ADC ta ce Atiku na iya lashe zaɓen shugaban ƙasa a Kano ko da Kwankwaso bai mara masa baya ba, tana mai cewa jama'a za su zabe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.