‘Yan Daban Siyasa Sun Kai Hari Ana Taron Jam’iyyar PDP, An Raunata Mata da Matasa

‘Yan Daban Siyasa Sun Kai Hari Ana Taron Jam’iyyar PDP, An Raunata Mata da Matasa

‘Yan dabar siyasar nan da aka fi sani da ‘Yan Kalare sun shiga gidan Salisu Abdulaziz a Gombe

  • Tun ba yau ba, ‘Yan ‘Yan Kalare sun yi kaurin-suna wajen rada rigimar siyasa a jihar Gombe da kewaye
  • Alhaji Salisu Abdulaziz ya ce an shigo masa gida ne a lokacin da suke taron ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP

Gombe - Akalla mutane biyar aka tabbatar an yi wa rauni a sakamakon harin da wasu da ake zargin ‘yan dabar siyasa ne su ka kai gidan wani mutum.

Rahotanni daga irinsu Daily Trust sun tabbatar da cewa wasu ‘yan iskan gari sun aukawa gidan Alhaji Salisu Abdulaziz a ranar Asabar a garin Gombe.

Salisu Abdulaziz wanda aka fi sani da Mr. B ya kasance cikin manyan ‘ya ‘yan APC mai mulki a yankin Jekadafari da ke Gombe, amma sai ya sauya-sheka.

Kara karanta wannan

Kaico: Daidai lokacin da zai kai 'ya'yansa makaranta, 'yan bindiga sun sheke lakcara a Anambra

Yayin da zai sanar da ficewarsa zuwa PDP, ‘Dan siyasar ya tara mata da matasa a gidansa da ke Jekadafari, ana wannan zama sai ‘yan daba suka duro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Yan Kalare a Jekadafari

Rahoton ya ce wadannan mutane sun tarwarsa taron siyasa bayan sun fasa kofar gidan Mr. B.

‘Dan siyasar ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin cewa an fasa fitilun kwai da wasu tagogin gidansa, kafin a kawo mahalarta taron da ake yi hari.

‘Yan Daban Siyasa
Jami'an tsaro Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jaridar Sun ta tuntubi ASP Mahid Mu’azu wanda yake magana da yawun bakin rundunar ‘yan sanda na reshen jihar Gombe a game da wannan lamari.

Mun kai su asibiti - Jibrin

ASP Mahid Mu’azu ya tabbatar da cewa abin ya faru, kuma mutane biyar sun samu rauni. Jami'in ya ce ‘yan sanda sun tattara su zuwa wani asibiti a garin.

Kara karanta wannan

N100m: An kashe 'yan sa kai a Arewa, Tinubu ya kwashi miliyoyin kudi ya ba iyalansu

Kakakin dakarun ‘yan sandan ya ce ba a cafke wadanda ake zargin su na da hannu a ta’adin ba tukun, amma ya tabbatar da cewa da karfi da yaji aka burma masu.

Rahoto ya bayyana cewa an shirya tsohon Gwamnan Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo zai ziyarci unguwar a lokacin da ‘Yan Kalare suka fado gidan.

A cewar Mr. B, ba komai ya jawo ya fice daga APC zuwa jam’iyyar PDP ba face rashin adalcin da ake yi a Gombe, shi kuma ya ga bukatar ya ceci jama’ar jihar.

Rantsarwa mu ke jira – Fashola

A rahoton da mu ka fitar a baya, an ji Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ya ce Peter Obi da Rabiu Kwankwaso za su hana Atiku Abubakar nasara.

Ganin 'yan takaran jam'iyyun LP, NNPP da kuma PDP duk su na tare a zaben 2019, duk da haka APC ta doke su, Fashola ya ce Bola Tinubu zai yi galaba a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel