Bayan Jefa Pantami a Matsala, Wanda Ya Nemi Takarar Gwamna a PDP Ya Koma APC

Bayan Jefa Pantami a Matsala, Wanda Ya Nemi Takarar Gwamna a PDP Ya Koma APC

  • Abdulkadir Hamma Saleh, tsohon ɗan takarar gwamnan Gombe a PDP, ya fice daga jam’iyyar ya koma APC gabanin zaɓen gwamna na 2027
  • Saleh ya fafata da Isa Ali Ibrahim Pantami neman tikitin PDP, wanda fuskantar ƙalubalen shari’a ya sa aka sake gudanar da zaɓen fidda gwani
  • Ya buƙaci magoya bayansa a faɗin Gombe su bi shi zuwa APC, su kuma goyi bayan ’yan takarar jam’iyyar a zaɓukan 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Abdulkadir Hamma Saleh, tsohon ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a Gombe, ya fice daga jam’iyyar adawa zuwa jam’iyyar APC mai mulki gabanin zaɓen gwamna na 2027.

Naija News ta ruwaito cewa Hamma Saleh, wanda ya fafata da tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami, neman tikitin takarar gwamnan PDP, ya sanar da sauya sheƙarsa cikin wata sanarwa da aka rabawa ’yan jarida a Gombe.

Kara karanta wannan

Takarar Pantami da hadu da sabon kalubale daga babban dan PDP

Bayan yanke shawarar komawa APC, tsohon ɗan takarar ya buƙaci magoya bayansa a faɗin jihar Gombe su bi shi zuwa jam’iyyar mai mulki, tare da goyon bayan ’yan takararta a zaɓukan 2027.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake takaddama kan tikitin takarar gwamnan PDP a jihar Gombe. An ƙalubalanci nasarar farko da Pantami ya samu a kotu, lamarin da ya kai ga sake gudanar da zaɓen fidda gwani.

Lamido ya ce PDP ce kaɗai ta tsira daga rugujewar jam’iyyun siyasa

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa PDP ce kaɗai jam’iyyar siyasa da ta tsira daga rugujewar sauran jam’iyyu tun bayan komawar Najeriya tsarin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.

Naija News ta ruwaito cewa Lamido, wanda yana daga cikin waɗanda suka kafa PDP, ya ce jam’iyyar ta ci gaba da wanzuwa duk da sauye-sauyen siyasa da aka samu tsawon shekaru.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a makomar Najeriya.

Ya bayyana hakan ne yayin bikin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen PDP a hedikwatar jam’iyyar ta jihar Jigawa da ke Dutse.

Kara karanta wannan

'Nadamar da APC za ta yi a ranar zabe': Kwankwaso ya jaddada kwarin guiwarsu

“Tun daga shekarar 1999, kusan dukkan jam’iyyun siyasa sun rushe, inda PDP ta kasance ita kaɗai jam’iyyar da har yanzu take nan daram.

“Ta ga jiya, tana ganin yau, kuma da yardar Allah za ta ga gobe,” in ji Lamido.

Tsohon gwamnan ya kuma buƙaci ’yan Najeriya da kada su sake maimaita abin da ya kira kuskuren zaɓen jam’iyyar APC a zaɓukan da suka gabata.

Ya yi kira ga masu zaɓe da su kwatanta ayyukan gwamnatocin PDP na baya da na gwamnatin APC mai ci yanzu kafin su yanke shawarar wanda za su goyi baya a babban zaɓen 2027.

“Ina ganin ’yan Najeriya sun koyi darasi daga kurakuransu. Saboda haka, ya kamata su yi nazari sosai kan nasarorin gwamnatocin PDP na baya, su kwatanta su da na gwamnatin yanzu kafin su yanke shawarar wanda ya kamata ya jagorance su.”

- In ji shi.

Lamido ya zargi gwamnatin APC mai ci da gaza cika muradun ’yan Najeriya, yana mai cewa ƙasar da jihar Jigawa suna buƙatar ƙwararrun shugabanni masu ƙwarewa domin magance matsalolinsu.

Kara karanta wannan

Magana ta bambanta: APC ta faɗi gaskiya kan rigimar Wike da gwamnoninta

Ya kuma soki yanayin harkokin lafiya da ilimi, yana zargin cewa waɗannan fannoni biyu sun tabarbare a ƙarƙashin gwamnatin yanzu.

“A yau, Jigawa na fuskantar manyan ƙalubale wajen samun ingantaccen kiwon lafiya. Asibitoci ba su da isassun ayyukan jinya da muhimman magunguna, yayin da harkar ilimi ke ci gaba da tabarbarewa."

- In ji shi.

Tsohon gwamnan ya tabbatar wa magoya bayan PDP cewa jam’iyyar a shirye take ta yi yaƙin neman zaɓen ’yan takararta a dukkan matakai a zaɓukan 2027, tun daga shugaban ƙasa zuwa Majalisar Dokoki ta Ƙasa da majalisun dokokin jihohi.

Ya kuma yi alƙawarin cewa yaƙin neman zaɓen jam’iyyar zai gudana cikin lumana, ba tare da zagi, barazana ko kai hare-haren magana kan abokan hamayyar siyasa ba.

Lamido ya ce babban burin PDP shi ne dawo da kyakkyawan shugabanci da kuma sake gina amincewar jama’a ga shugabannin siyasa.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.