2027: Tinubu Ya Yi Kira ga Majalisa bayan Nada Sababbin Mukamai a INEC
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sababbin kwamishinonin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) guda shida domin maye gurbin waɗanda wa’adin aikinsu ya ƙare
- Mutanen da aka naɗa sun haɗa da kwamishinonin ƙasa huɗu da kwamishinonin zaɓe na jihohi biyu, waɗanda Majalisar Dattawa za ta tantance kafin tabbatar da naɗinsu
- Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta gaggauta tantance mutanen domin shirye-shiryen babban zaɓen da za a gudanar a watan Janairun 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sababbin kwamishinonin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) guda shida domin cike guraben da suka samu sakamakon ƙarewar wa’adin wasu jami’an hukumar.
Hakan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen zaben shugaban kasa na shekarar 2027, inda jam'iyyu ke kamfen a Najeriya.

Source: Facebook
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Facebook.
Sunayen sabbin kwamishinonin
Sababbin kwamishinonin ƙasa uku da aka naɗa sun haɗa da Farfesa Mustapha Aliu, wanda zai wakilci yankin Arewa maso Yamma, inda zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Zuru.
Na biyu shi ne Bashir Muhammed Umar, wanda zai wakilci Arewa ta Tsakiya, inda zai maye gurbin Farfesa Muhammad Adamu.
Haka kuma, Tinubu ya naɗa Misis Oluwatoyin Babalola a matsayin kwamishiniyar ƙasa mai wakiltar Kudu maso Yamma.
A halin yanzu, ita ce kwamishiniyar zaɓe mazauniyar INEC a jihar Osun, kuma za ta maye gurbin Farfesa Cornelius Ajayi, wanda wa’adinsa zai ƙare ranar 24 ga Oktoba.
An naɗa kwamishinonin zaɓe a jihohi
Shugaban ƙasar ya kuma naɗa Dokta Samuel Akinjide Akinleye, tsohon babban sakatare a gwamnati mai ritaya, a matsayin kwamishinan zaɓe mazauni na jihar Ekiti.
Ɗayan wanda aka naɗa shi ne Zahradden Basiru Sanusi daga jihar Jigawa, wanda zai maye gurbin Farfesa Saidu Ahmed Babura.
Sanarwar fadar shugaban ƙasa ta kuma bayyana cewa Tinubu ya sake naɗa Dr Bala Bila, kwamishinan ƙasa mai wakiltar Arewa maso Gabas, domin ci gaba da aikinsa.

Source: Facebook
Tinubu ya nemi a tantance su
A cewar Onanuga, Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta hanzarta tantance mutanen da aka naɗa saboda zaɓukan da ake shirin gudanarwa a watan Janairu.
Punch ta wallafa cewa sanarwar ta ce:
“Shugaba Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta gaggauta tabbatar da naɗin mutanen bisa la’akari da babban zaɓen da za a gudanar a watan Janairu mai zuwa.”
NDC ta yi kwa INEC korafi
A wani labarin, kun ji cewa 'yan Kwankwasiyya sun gudanar da zanga-zanga a Kano ranar Juma’a, inda suka nemi a dawo da sunan ɗan takarar gwamnan jam’iyyar NDC, Aminu Gwarzo, cikin jerin sunayen ’yan takara.
Mataimakin ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar, Mustapha Rabiu Kwankwaso, ne ya jagoranci masu zanga-zangar zuwa ofishin INEC na jihar, inda suka miƙa takardar ƙorafi.
Kwamishinan INEC a Kano, Abdu Zango, ya tabbatar da karɓar ƙorafin, inda ya ce hukumar ta riga ta bayyana dalilin rashin sunan, amma har yanzu akwai damar ɗaukaka ƙara har zuwa ranar 24 ga Oktoba.
Asali: Legit.ng

