Za a Ginawa Talakawa Gidaje 100 a Kowace Karamar Hukumar Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin gina gidaje 100 na tallafi a kowace ƙaramar hukuma a Najeriya domin rage ƙarancin gidaje da kuma sauƙaƙa wa ’yan ƙasa samun matsuguni
- Ministan Gidaje da Raya Birane, Muttaka Rabe Darma, ya ce gwamnati na kuma duba yiwuwar ƙara iyakar lamunin sayen gida daga N50m zuwa N85m
- Ya kuma bayyana shirin samar da tsarin lamunin gidaje mai sauƙi, musamman ga ma’aikata masu ƙaramin albashi da ’yan Najeriya da ke aiki a ɓangaren sana’o’in hannu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto – Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin gina gidaje 100 na tallafi a kowace ƙaramar hukuma a faɗin Najeriya domin rage matsalar ƙarancin gidaje da kuma bai wa masu ƙaramin ƙarfi damar mallakar matsuguni.
Ministan Gidaje da Raya Birane, Muttaka Rabe Darma, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, yayin rufe taron Majalisar Ƙasa kan Filaye, Gidaje da Raya Birane karo na 15 da aka gudanar a jihar Sokoto.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa Darma ya kuma bayyana cewa gwamnati na duba yiwuwar ƙara iyakar kuɗin lamunin sayen gida daga N50m zuwa N85m domin taimaka wa ’yan Najeriya su mallaki gidaje duk da hauhawar kuɗin gine-gine.
Gidajen da gwamnati za ta gina
Ministan ya ce shirin gidaje na tallafi zai fi mayar da hankali kan mutanen da ke samun ƙaramin albashi, musamman ma’aikatan da ba su da ikon gina gidajensu ko sayen na kansu.
Ya ba da misalin malaman makarantun firamare da sauran ma’aikatan da ke shafe tsawon rayuwarsu suna haya, yana mai cewa gwamnati na son tabbatar da cewa masu ƙaramin kuɗin shiga ma za su iya samun gidaje masu inganci a farashi mai sauƙi.
Darma ya ce gwamnati ta kuma umarci Bankin Lamunin Gidaje na Najeriya da ya ware aƙalla kashi 70 cikin 100 na kuɗin da yake tara wa a kowace shekara domin tallafa wa lamunin sayen gidaje.

Kara karanta wannan
Magana ta fito daga bakin minista, an ji adadin shekarun da Tinubu ke buƙata a kan mulki
Ya ƙara da cewa ana aiki kan kafa Hukumar Kuɗin Gidaje ta Ƙasa domin ƙarfafa sa ido, haɗin gwiwa da riƙon amana a fannin samar da kuɗin gidaje.
Za a sauƙaƙa wa ’yan Najeriya
Darma ya bayyana cewa gwamnati na shirin faɗaɗa damar mallakar gidaje ga ’yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje ta hanyar wani shirin lamunin gidaje da zai ba su damar mallakar gidaje a wuraren da suka zaɓa.
Ya kuma ce ana samar da tsarin kula da bayanan filaye na bai ɗaya domin bai wa masu son sayen filaye damar tabbatar da masu mallakarsu da kuma gano ko akwai takaddamar shari’a a kansu ba tare da zuwa jihohin da filayen suke ba.

Source: Original
An raba tallafi a Sokoto
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya cika alƙawarin tallafa wa ’yan kasuwa 76 da gobara ta shafa a Tsohon Kasuwar Sokoto da tashar mota ta Central Motor Park.
Gwamnan ya bayar da tallafin N143m ga ’yan kasuwar da aka tantance a matsayin waɗanda gobarar ta shafa da gaske, domin taimaka musu su farfaɗo da harkokin kasuwancinsu.
Shugaban kwamitin, Gandi Umar Muhammad, ya bayyana cewa kuɗin ba diyya ba ne, sai dai tallafin da aka bayar domin taimaka wa waɗanda abin ya shafa su sake farfaɗo da kasuwancinsu.
Asali: Legit.ng
