2027: Hadiman Tinubu za Su Shigo Wasu Jihohin Arewa Jin Ra'ayoyin Talakawa

2027: Hadiman Tinubu za Su Shigo Wasu Jihohin Arewa Jin Ra'ayoyin Talakawa

  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce talakawan Najeriya sun fara amfana da sauye-sauyen da Bola Tinubu ya kawo
  • Hadimin shugaban kasar ya ce jama'a da dama a yankunan da ya ziyarta domin duba abubuwan da ke faruwa suna yabon shugaba Tinubu
  • Onanuga ya bayyana cewa jihohi sun samu ƙarin kuɗi a kakashin gwamnatin Bola Tinubu domin aiwatar da ayyukan raya ƙasa masu yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya ce talakawan Najeriya sun fara amfana da sauye-sauyen da aka yi a kasar nan.

Onanuga ya yi magana yana mai nuni da ayyukan gine-gine, shirye-shiryen tattalin arziki da ayyukan ci gaba da ake gudanarwa a jihohi daban-daban a matsayin hujjar cewa ƙasar na tafiya a hanya mai kyau.

Kara karanta wannan

Shawarar da tsohon shugaban kungiyar CAN ya ba Tinubu kan sake takara a 2027

Bayo Onanuga da Bola Tinubu
Bayo Onanuga a hagu da Bola Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Hadimin shugaban kasar ya yi bayanin ne a wata hira da tashar Arise News domin tattauna wasu nasarorin da Bola Tinubu ya samu a Najeriya.

'Talakawa na yabon Tinubu' Onanuga

Bayo Onanuga ya ce shugaban kasar na samun yabo ne yayin da yake mayar da martani ga kalaman Peter Obi na cewa ya kamata Tinubu ya yi murabus.

Ya jaddada cewa ƙarin goyon bayan da jama'a ke nuna wa gwamnati alama ce ta yadda suke yaba ƙoƙarin da gwamnatin ke yi wajen inganta rayuwarsu da ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce:

“Mun dawo ne makon da ya gabata daga rangadi a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, kuma yanzu muna shirin zuwa Arewa maso Yamma.
"Mun yi magana da talakawan Najeriya kuma suna yabon shugaban ƙasa. Jama'a suna yabon shugaban kasa."

Magana kan tsadar rayuwa

Duk da amincewa da cewa tsadar rayuwa ta ƙaru, Onanuga ya ce waɗannan ƙalubale na daga cikin wahalhalun da ake fuskanta yayin aiwatar da manyan sauye-sauyen tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Yadda aka nemi ceto malamar Islamiyya amma mutane suka taru suka kashe ta

Ya bayyana cewa gyara manyan lamuran da suka shafi tattalin arziki yana da muhimmanci domin samun ci gaba mai ɗorewa a nan gaba.

Ya ce:

“Ba na cewa babu ƙarin tsadar rayuwa. Amma abin da nake cewa shi ne halin da ake ciki bai kai yadda 'yan adawa ke bayyanawa ba."

Da ya ke martani kan wahalar da ake sha, Onanuga ya kuma ce bai ga irin matsananciyar yunwar da wasu 'yan Najeriya ke korafi a kai ba.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Bola Tinubu yayin wani jawabi a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya ce yana da ma'aikata da ke yi masa aiki a kashin kansa kuma yana tambayarsu yadda suke rayuwa da yanayin tattalin arzikin da ake ciki.

Ga bidiyon da Onanuga ya yi magana a kasa:

Ma'aikata sun ce ana wahala

A wani labarin, kun ji cewa ma'aikatan Najeriya sun yi korafi da cewa mafi karancin albashin da ake biyan su a yanzu ya yi kadan sosai.

Yayin wani taro da suka yi a jihar Osun, kungiyar ma'aikata ta yi kira ga gwamnatin tarayya da jihohi da su kara albashi da kashi 40.

Ta bayyana cewa hakan ya zama wajibi domin N70,000 ba ta iya daukar nauyin ma'aikaci yadda ya kamata lura da halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng