An Sanya Sheikh Daurawa da Wasu Manyan Malaman Musulunci 3 a Kwamitin Kamfen APC
- Jam’iyyar APC a Kano ta fitar da sunayen mambobin kwamitin ba da shawarwari kan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna gabanin zaɓen 2027
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ne zai jagoranci kwamitin, yayin da mataimakinsa, Murtala Sule Garo, zai zama mataimakin shugaban kwamitin
- Daga cikin waɗanda aka sanya akwai fitattun malaman addinin Musulunci, ciki har da Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - A wani mataki da ba a yi tsammani ba kuma bai ba mutane mamaki ba, an ga sunayen fitattun malaman musulunci a kwamitin da aka kafa domin ba da shawarwari kan yakin neman zaben APC a Kano.
Tun farko dai jam’iyyar APC a Jihar Kano ta fitar da sunayen mambobin kwamitin ba da shawarwari kan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan
Wajen rantsar da kwamitin kamfe ya zama matattarar habaici tsakanin Akpabio, Wike da gwamnoni

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sunayen ya ƙunshi fitattun malaman addinin Musulunci, shugabannin siyasa da jami’an gwamnati daga jihar.
Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana cewa shugaban APC na jihar, Hon. Umar Haruna Doguwa, ne ya fitar da jerin sunayen.
Gwamna Abba Kabir Yusuf zai jagoranci kwamitin, yayin da mataimakinsa, Murtala Sule Garo, zai zama mataimakin shugaban kwamitin.
Malaman addinin da aka zaɓa
Daga cikin malaman addinin Musulunci da aka sanya a kwamitin akwai tsohon shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) kuma shugaban kungiyar Izala ta Kano, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan.
Sauran sun haɗa da kwamandan hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa; Sheikh Ali Dan Abba, kwamishina na dindindin a Hukumar Shari’a ta Jihar Kano; da kuma fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Nazifi Bichi.
Manyan ’yan siyasar da ke kwamitin
Jerin sunayen ya kuma ƙunshi manyan ’yan siyasa, ciki har da tsoffin gwamnoni Dr Abdullahi Umar Ganduje, Sanata Kabiru Gaya da Malam Ibrahim Shekarau.
Sauran sun haɗa da mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin; ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Bichi, Abubakar Kabir Bichi; Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila; da Sanata Rufai Sani Hanga, da sauransu.

Source: Facebook
Wani mazaunin Hotoro a cikin birnin Kano, Muhammad Sani ya shaida wa Legit Hausa cewa ba abin mamaki bane don an ga irinsu Daurawa da Pakistan a cikin kwamitin kamfen APC.
A cewarsa, Sheikh Daurawa na cikin jami'an gwamnatin Kano kasancewarsa kwamandan Hisbah, haka kuma Pakistan tsohon shugaban NAHCON ne wanda ya yi aiki da Tinubu.
"Muna wa malamanmu fatan alheri a kowane abu da suka tasa a gaba, batun koyarwar addini daban, harkokin siyasa daban, don haka ba ko'ina ba ne za mu masu biyayya amma muna kyautata masu zato," in ji shi.
APC ta rasa babban jigo a Kano
Kun ji cewa tsohon shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA), Aminu Dabo, ya yi murabus daga jam'iyyar APC nan take.
Aminu Dabo ya ce ya yanke wannan shawara ne bayan yin nazari sosai kan wasu dalilai na kansa da kuma abubuwan da yake shirin cimmawa a nan gaba.
Asali: Legit.ng
