Kwana Ya Kare: Tsohon Shugaban FRSC Ta Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Kwana Ya Kare: Tsohon Shugaban FRSC Ta Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Hukumar FRSC ta yi jimamin rasuwar tsohon shugabanta, Dauda Ali Biu, inda ta bayyana shi a matsayin jami’i mai kishin aiki da ladabi
  • Dauda Biu ya zama shugaban hukumar na bakwai a watan Yulin 2022, kuma ya riƙe muƙamin har zuwa watan Mayun 2024
  • FRSC ta ce gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa harkokin kiyaye lafiyar masu amfani da hanya za ta ci gaba da kasancewa cikin tarihin hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da rasuwar tsohon shugabanta, Dauda Ali Biu, inda ta bayyana matukar kaduwarta kan wannan babban rashi.

FRSC ta bayyana marigayin a matsayin jami’i mai kishin aiki da ladabi wanda ya bayar da gagarumar gudummawa wajen gudanar da harkokin kiyaye lafiyar masu amfani da hanya da kuma ci gaban hukumar.

Kara karanta wannan

'Yan Kwankwasiyya a Kano sun tafi ofishin INEC kan cire sunan Aminu Gwarzo

Dauda Biu.
Tsohon shugaban hukumar FRSC ta Najeriya, Dauda Ali Biu lokacin yana bakin aiki Hoto: Nafi'u Isa Zannah
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin saƙon ta’aziyyar da hukumar FRSC wallafa a shafinta na X ranar Litinin, 12 ga watan Oktoba, 2026.

FRSC ta yaba da aikin Dauda Biu

Shugaban FRSC na kasa, Shehu Mohammed, ya ce rayuwar aikin Dauda Biu ta kasance cike da jajircewa, ladabi da kuma ci gaba da sadaukar da kai ga hidimar jama’a.

Dauda Biu, wanda ya shiga FRSC a shekarun farko na kafuwar hukumar, ya samu karin girma zuwa matakai daban-daban har ya zama shugaban hukumar na bakwai da aka naɗa bisa cikakken tsari.

Ya riƙe muƙamin shugaban FRSC ta Najeriya daga watan Yulin 2022 zuwa watan Mayun 2024.

Gudummawar Dauda Biu a FRSC

Mohammed ya ce marigayin ya nuna zurfin fahimtar aikin da aka kafa hukumar domin gudanarwa a tsawon shekarun hidimarsa, inda ya bayar da gudummawa wajen ƙarfafa tsarin kula da lafiyar masu amfani da titi.

Ya ce shugabancin Dauda Biu ya ba shi matsayi na musamman a tarihin hukumar, yana mai cewa gudummawar da ya bayar ta ci gaba da kasancewa wani ɓangare na gadon ayyukan da FRSC ke alfahari da su.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya zafafa da ya kwatanta Tinubu da dakikin dalibi

“Gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa da ci gaban FRSC ta ci gaba da kasancewa wani ɓangare na nasarorin da muka gada, waɗanda muke ci gaba da ginawa a kansu,” in ji Mohammed.

FRSC ta mika sakon ta'aziyya

Shehu Mohmmed ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayin na kusa, abokansa, abokan hulɗarsa da sauran waɗanda rasuwarsa ta shafa.

“A madadin shugabancin da daukacin ma’aikatan FRSC, ina miƙa ta’aziyyata mafi zurfi ga iyalansa na kusa, abokansa, abokan hulɗarsa da duk waɗanda ya taɓa rayuwarsu.
“Muna tare da su a wannan lokaci na baƙin ciki, kuma muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba su ƙarfin jure wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba,” in ji shi.
FRSC.
Dauda Ali Biu yana gaiswa da jami'ai a lokacin yana matsayin shugaban hukumar FRSC a 2024 Hoto: FRSC Nigeria
Source: Facebook

Kakkin hukumar kashe gobara ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya riga mu gidan gaskiya.

Jami'an hukumar kashe hobara da suka yi aiki tare da shi sun fara bayyana alherin marigayin tare da amincewa da gudunmawar da ya bayar wajen kare lafiyar jama’a

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262